Shirye-shiryen zaɓe a ƙasar Guinea | Siyasa | DW | 23.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirye-shiryen zaɓe a ƙasar Guinea

A ranar lahadi mai zuwa ne ake shirin gudanar da zaɓe a ƙasar Guinea

default

Shirin zaɓe a ƙasar Guinea

A daidai lokacin da ya rage kwanaki huɗu a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Guinea Conakry, magaoya bayan 'yan takara daban daban sun fara zaman ɗarɗar sakamakon hasashen tashe tashen hankali da ka iya ɓarkewa a lokacin kaɗa ƙuri'a.

Kusan ko ta ina aka bi a Conakry da ma dai sauran manyan birne na Guinea ba abin da ake gani illa hotunan 'yan takara da muradun da suke son cimma idan suka ɗare kan kujera. A ɗaya hannun kuma magoya bayan 'yan takaran ne ke bushe bushe a kan tituna a duk lokacin da gwanayen nasu ke gudanar da gangamin siyasa. Ɗoki da murna da ɓangarori daban daban ke nunawa, ya sa ake fuskantar ruɗani daga wannan ɓangare na Guinea i zuwa wancan. Ko shi ma Ibrahima Ndiaye wani ɗan jaridan Guinea da ya halarci wani taro a nan Bonn,sai da ya danganta wannan da azarɓaɓbin sabon shiga ga tsarin jaririyar demoƙaraɗiya da Guinea ke neman runguma. Ya dai ƙara da bayani yana mai cewar:

"Wannan alhakkin ya rataya ne a kawunan darektocin yaƙin neman zaɓe na 'yan takara . Ba sa amfani da gangamin da suke shiryawa domin sanar da al'uma tare da faɗakar da su illar da ke tattare da rikice-rikicen siyasa. Ka ga dole a sami tashe-tashen hankula. Halin da ake ciki na nunawa cewa har yanzu ƙasarmu ba ta fahimci ɗaukacin shika-shikan tafarkin demoƙaraɗiya sosai ba."

sai dai al'umar ƙasar ta Guinea na danganta zaɓen na ranar lahadi da zama zakaran gwajin dafi na sabuwar alƙiblar 'yanci da walwala da Guinea za ta fuskanta. Dalili kuwa shi ne ƙasar ta jima tana fuskantar mulkin kama karya da kuma na soja da ya sa ta yin ƙaurin suna a duniya. To amma Ibrahima Ndiaye na rediyon Nostalgie ya ce ba ya ganin cewa zaɓen wannan karon zai bai wa Guinea damar juya babin cin zarafin 'yan siyasa da kuma na faɗin albarkacin baki.

"Ya kamata a ƙalubalanci al'umar Guinea game da wannan zaɓe. Bai kamata a yi hasashen cewa komai zai tafi salin alin ba. Zai yi wuya a ce an tashi daga mulkin kama karya i zuwa demoƙaraɗiya ba tare da fuskantar wata hatsaniya ba. Ayar tambaya a nan ita ce, wai shin 'yan Guinea sun kintsa domin ganin cewa sun rungumi tafarkin demoƙaraɗiya ba tare da tayar da hatsaniya ba."

Mawallafi: Muhammed Awal Balarabe

Edita: Ahmad Tijani Lawal