Shirye shiryen taron kungiyar kasashen musulmi na dunia a Saudiyya | Labarai | DW | 06.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirye shiryen taron kungiyar kasashen musulmi na dunia a Saudiyya

Gobe ne idan Allah ya kai mu a birninJidah na Saudi Arabia,a ke buda taron shugabanin kasashen membobin kungiyar kasashen musulmi ta dunia wato OCI.

A jajibirin wannan mahimin taro Sarki Abdallah mai masabkar baki, ya gayaci mahalarta taron, da su zo da cikkakun shawarwari, na kara daukaka martabar addinin musulunci a dunia, da kuma kare shi, daga mumunar fahimtar da wasu ke yi masa, ta hanyar dangata shi da ta´adanci.

Wajibi a cewra sa kasashen usulmi su hada kai dominfuskantar kalu bale na dunia.

Kungfiyar OCI ta kunshi kasashen musulmi 57 na dunia.