1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirye-shiryen taron ƙoli tsakanin Sin da Afrika

Gobe idan Allah ya kai mu, za a buɗe babban zaman taro, tsakanin hukumomin ƙasar Sin, da takwarorin su, na nahiyar Afrika.

A jimilce, a na sa ran shugabani a ƙallla 40, na Afrika za su halarci taron.

A halin yanzu, tunni shugabani da dama, da su ka haɗa da Abdoul Aziz Bouteflika na Algeria, da Omar El Beshir na Sudan, sun riga sun sauka a birnin Bejing.

Kakakin opishin ministan harakokin wajen China, Liu Jianchao, ya ce burin wannan taro, shine ƙara ƙarfafa daƙon zumuci, ta fanin tattalin arziki, da diplomatia, tsakanin China da ƙasashen Afrika.

Sophie Greney ,wani massani ne, ta fannin harakokin saye da sayarwa, tsakainin Afrika da China, ya nazari a game da wannan hulɗodi.

A jajibirin buɗe wannan mahiman taro, hukumar kare haƙoƙin bani adama, Amnisty International, ta yi kira, ga hukumomin Pekin ,su yi anfani da wannan dama, domin tantanawa, da shugabanin, Sudan da Zimbabwe, a game da uƙubar da jama´ar ke sha a wannan ƙasashe.