1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen sake zaɓe a Jihar Agadez

March 22, 2011

Ƙwararru ta fannin Dokar ƙasar Nijar na cigaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da waɗanda ke shirin yin takara a zaɓuɓɓukan da aka soke

https://p.dw.com/p/10foC
Hoto: DW

A janhuriyar Nijar  mahawara  ta kuno kai tsakannin Masana illimin doka akan maganar zaɓen 'yan Majalisun dokoki da za a sake gudanarwa a cikin jihar Agadez da ke a yankin arewaci na ƙasar.

Hakan kuwa ya biyo bayan kura kuran da kotun tsarin mulkin ta dago kan cewar wasu yan takara jam'iyyar na PNDS tarayya sun yi amfani da takardu na gogi a zaben farko

Ana sa ran dai shugaban jam'iyyar MNSD Nasara Seyni Omar da Mahaman Ousman shugaban jam'iyyar CDS rahama wanda basu da Kujeru a  sabuwar Majalisar  dokokin za su sake tsayawa takara  a zaɓen  na cike gurbi. Wakilimmu Gazali Abdou Tasawa ya aiko mana da rahoto dangane da wannan mahawara da ke gudana a Janhuriyar ta Nijar.

Edita: Zainab Mohammed Abubakar