Shirye shiryen kafa sabuwar gwamnati a Jamus | Siyasa | DW | 29.09.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirye shiryen kafa sabuwar gwamnati a Jamus

A ranar tara ga watan nuwamba mai zuwa ne shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke fatan naɗa sabuwar gwamnatin haɗin guiwa tare da jam'iyyar Free Democrats sakamakon nasarar da ta samu a zaɓen ranar lahadi da ta wuce.

default

Angela Merkel, shugabar gwamnatin Jamus da Guido Westerwelle, shugaban jam´iyar FDP

A daidai wannan ranar ce za a cika shekaru 20 da rushewar katangar Berlin.

Wajibi ne dai 'yan Christian Union dake da ra'ayin mazan jiya da 'yan Free Democrats dake da sassaucin manufofin siyasa su shiga tattaunawa akan gwamnatinsu ta haɗin guiwa a cikin makonnin nan masu zuwa saboda su kawar da dukkan abubuwan da ka hana ruwa gudu ga ayyukan gwamnatinsu. Domin kuwa akwai banbance-banbancen ra'ayi da dama tsakanin sassan biyu, misali game da manufofin kuɗi da na tsaro. A halin da ake ciki yanzu haka basusuka su kai wa Jamus iya wuya, kuma gwamnati na shawarar karɓar ƙarin rancen Euro miliyan dubu ɗari shekara mai zuwa. Amma duk da haka 'yan Christian Union da 'yan Free Democrats sun yi wa jama'a alƙawarin sassaucin haraji a matakansu na yaƙin neman zaɓe. Guido Westerwelle, shugaban jam'iyyar Free Democrats na fatan ganin an ɗauki matakan gaggawa don yi wa jama'a da kuma ƙananan kamfanoni sassauci:

"Har yau muna kan bakanmu na cewar kamanta adalci akan haraji shi ne babban sharaɗin daidaita baitul-malin gwamnati."

Bisa ga ra'ayin Westerwelle dai rangwamen harajin zai taimaka wajen sake ta da komaɗar tattalin arziƙin ƙasa saboda jama'a zasu samu isasshen kuɗin sayayya, wanda ta haka zai taimaka gwamnati ta samu ƙarin kuɗaɗen shiga sakamakon sabbin guraben aikin yi da za'a ƙirƙiro. To sai dai kuma akwai masu tababa game da hakan kamar dai shugaban cibiyar binciken tattalin arziƙin Jamus Klaus Zimmermann wanda ke ba da shawarar ƙara yawan harajin hajoji daga kashi 19 a yanzu zuwa kashi 25%. Shi kansa wannan harajin sai da tsofuwar gwamnatin da aka naɗa bayan zaɓen shekara ta 2005 tayi ƙarin kashi uku cikin ɗari kansa saboda ta daidaita baitul-malinta. A wancan lokaci an fuskanci mawuyacin hali makamancin wanda ake ciki yanzun, kuma ta la'akari da haka ne shugabar gwamnati Angela Merkel ke ɗariɗari game da sanya wata rana ta sassacin harajin. Bisa ga ra'ayinta, muhimmin abu a yanzun shi ne zayyana kasafin kuɗin shekara mai zuwa ta 2010.

"Muhimmin abin dake gabanmu a yanzun shi ne mu yi bakin ƙoƙarinmu wajen samar da bunƙasar tattalin arziƙi, saboda ita ce zata samar da sabbin guraben aiki ga jama'a. Kuma wannan shi ne babbar manufarmu."

Ɗaya matsalar da wajibi ne kuma jam'iyyun na Christian Union da Free Democrats su cimma daidaituwa kanta kuma ita ce ta tsaro. Domin kuwa jam'iyyar Free Democrats ta sha ƙalubalantar dokoki da dama na tsaro da aka gabatar ƙarƙashin gwamnatin haɗin guiwa ta Christian Union da Social Democrats. Kazalika akwai saɓani a tsakaninsu game da manufofin tsaron kan ƙasa. Domin kuwa Free Democrats ta daɗe tana neman ganin a gusar da makaman ƙare dangin da aka ɗirke a harabar Jamus zamanin yaƙin cacar baka. Kazalika Westerwelle na goyan bayan mayar da aikin soja bisa son rai. To ko yaya al'amura zasu kasance sai dai a zuba na mujiya a ga salon kamun ludayin shugaban na Free Democrats, a matsayinsa na sabon ministan harkokin wajen Jamus. Muƙamin da ba shakka Westerwelle zai kama, ko da yake ba a shiga tattaunawa akan rabon muƙamai ba tukuna.

Mawallafa: Marcel Fürstenau / Ahmed Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal