Shirye-shiryen girka sabuwar gwamnati a Palestinu | Labarai | DW | 07.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirye-shiryen girka sabuwar gwamnati a Palestinu

A yau ne shugaban kungiyar Jihadil Islami na Naplouse a Palestinu, Ahmad Radad,ya rasa ransa, a cikin wata mansayar wuta da dakarun kasar Isreala.

Dakarun Isreala na tuhumar sa ,da kitsa harin kunar bakin waken ranar 19 ga watan Janairu,da ya wuce, a birninTel Aviv, wanda ya hadasa mutuwar mutane 19.

A nata gefe kungiyar Hamas, da ta samu gagaramar nasara a zaben yan majalisu dokokin Palestinu, ta fara shirye shiryen girka sabuwar gwamnati.

A sakamakon wata ganawa da ta hada hukumar tsaron kasar Masar, da tawagar kungiyar Hamas, sun cimma daidaito akan girka gwamnatin hada ka, da za ta kunshin ya kungiyar Fatah, da ta sha kasa, a wannan zabe.

Saidai ya zuwa yanzu, da dama daga kusoshin kungiyar Fatah, sun bayyana kin amincewa, da shiga wannan gwamnati.

Shugaban hukumar Palestinawa, Mahamud Abbas, da ya fara ziyara aiki a yau, a kasar Koweiti, ya ki cewa yan jarida uffan, a game da batun.