Shirye-shiryen binne Muhammad Ali
June 6, 2016Talla
Ana sa ran mashahuran mutane za su hallara a jawabai da za a yi domin tuna wa da shahararran tsohon dan damben duniya Muhammad Ali. Daga cikin manyan bakin da za su yi jawabi har da tsohon shugaban Amirka Bill Clinton da kuma dan wasan barkwanci Billy Crystal.
Shi dai Muhhammad Ali ya bar duniya yana da shekaru 74 da haihuwa, kuma ya kasance cikin shahararrun mutane a karni na 20 da ya gabata. Mutane da dama a duniya sun nuna juyayi da mutuwar ta Muhammad Ali.