Shirye-shiryen aika rundunar EU a Tchad da RCA | Labarai | DW | 14.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirye-shiryen aika rundunar EU a Tchad da RCA

Ƙungiyar taraya Turai ta tura tawagar sojoji a ƙasar Tchad a shirye shiryen aika rundunar shiga tsakani a wannan ƙasa da kuma maƙwabciyar ta, Jamhuriya Afrika ta tsakiya.

Wannan tawaga da ta ƙunshi sopjoji 40 na EU na da yaunin tantanawa da hukumomin N´Djamena, a game da matakan aika rundunar, musamman, yankuna da za ta girka sasani, da kuma irin tallafin gwamnatin Tchad ga wannan sojojin kiyaye zaman lahia.

Rundunar ta ƙungiyar taraya Turai, za gudanar da ayukan tsaro, ga dubunan yan gudun hiijira na yankin Darfur a ƙasar Sudan, wanda su ka sami matsugunai a ƙasashenTchad da Jamhuriya Afrika ta tsakiya.

Ranar 25 ga watan da ya gabata, komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia, ya kada kuri´ar amincewa da zaman sojoji EU, su kimanin dubu 3, a ƙasashen Tchad da Jamhuriya Afrika ta tsakiya.

A wata mai kamawa na November, a ke kyautata zaton fara aika rukunin farko, na wannan runduna.