Shirin zaman lafiya tsakanin Israila da Palasɗinawa. | Labarai | DW | 24.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin zaman lafiya tsakanin Israila da Palasɗinawa.

P/M Israila Ehud Olmert yace a shirye yake domin tattauna shirin zaman lafiya da Palasdinawa, amma idan har sun ƙi amincewa, to Israila za ta yi gaban kan ta wajen shata kan iyakar ta a gaɓar yamma da kogin Jordan. Olmert wanda ya baiyana hakan ga taron manema labarai a birnin Washington, yace ba za su cigaba da bata lokaci wajen sauraron Palasɗinawa ba, yana mai cewa babban fatan su, shi ne samawa yankin su kyakyawar makoma ta hanyar zaman tare da Palasɗinawa. Ehud OLmert wanda ya yi jawabi ga yan majalisar dokokin Amurka ya sanar da cewa janye matsugunan yahudawa daga gabar yamma abu ne mai muhimmanci ga tsaron ƙasar Israila. Ya kuma jinjinawa Amurka bisa gudunmawar da take baiwa Israila. yace cigaban shirin wanzar da zaman lafiyar ba zai yiwu ba batare da gudunmawar Amurka ba. A wani matakin sauyin manufa, fadar white House ba zato ba tsammani ta bayar da goyon baya ga shirin Israila na shata kan iyakar ta gaba gaɗi, idan shugabannin Hamas suka ki ajiye makaman su da kuma akidar ganin bayan ƙasar Israila.