1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin zaman lafiya a Yankin Gabas Ta Tsakiya

Anyi taho mu gama a tsakanin ´yan jam´iyyar Fatah ta Mahmud Abbas da kuma ´yan ƙungiyyar Hamas a Gaza. Hakan ya haifar da asarar rayuka shidda, a hannu ɗaya kuma da jikkatar wasu 30. Al´amarin yazo ne bayan Mr Abbas ya ƙara nanata aniyarsa na gudanar da zaɓe ne a yankin. A jawabinsa na bikin cikar Jam´iyyar ta Fatah shekaru 43, Mr Abbas ya ce hakan zai kawo ƙarshen rikice-rikice da tashe-tashen hankula a yankin. Bugu da ƙari shugaban ya kuma buƙaci yin sulhu a tsakanin ɓangarorin biyu. Samun hakan a cewar Abbas, abune da zai taimaka, wajen samun sauƙin warware rikicin dake tsakanin yankin da Israela.