1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisu a Afirka

Ahmed Salisu/ LMJMarch 18, 2016

Za a gudanar da zabuka zagaye na biyu a wasu kasashen Afirka ya yin da wasu kumaza su gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu, har ma da zaben raba gardama.

https://p.dw.com/p/1IG3Y
Masu kada kuri'a a rumfar zabe
Masu kada kuri'a a rumfar zabeHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

A ranar Lahadin da ke tafe ne za a yi zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Nijar da kuma Jamhuriyar Benin, kana za a gudanar da zagaye na biyu na zabuka a Tsibirin Zanzibar. A kasar Kongo kuwa zaben shugaban kasa za a gudanar kana a Tsibirin Capeverde a gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki. Al'ummar kasar Senigal kuwa zaben raba gardama za su gudanar.

Gangamin yakin neman zabe a zagaye na biyu a Nijar
Gangamin yakin neman zabe a zagaye na biyu a NijarHoto: I. Sanogo/AFP/Getty Images

Nijar takara tsakanin Issufou da Hama

A Jamhuriyar Nijar dai shirye-shirye sun kankama, na gudanar da zabuka zagaye na biyu tsakanin Shugaba Mouhamadou Issufou na jam'iyya PNDS da ke neman wa'adi na biyu da kuma dan takarar jam'iyyar adawa ta Lumana Afirka Hama Amadou wanda ke tsare a gidan kaso sakamakon zarginsa da hannu a wata badakalar cinikin jarirai. A yanzu dai an fitar da Hama Amadou zuwa wani asibiti a kasar Faransa domin duba lafiyarsa. Hukumar zaben kasar CENI dai ta sha alwashin gudanar da zaben a karshen mako, duk kuwa da barazanar kaurace masa da jam'iyyun adawar kasar baki daya suka yi.

Benin zagaye na biyu na zaben shugaban kasa

A Benin kuwa za a gudanar da zagaye na biyu na zaben ne tsakanin hamshakin attajirin nan Patrice Talon da kuma firaministan kasar Lionel Zinsou. Masu kada kuri'a a kasar ta Benin mai yawan al'umma kimanin miliyan goma za su maida hankali ne kan zaben mutum guda daga cikin 'yan takarar biyu da za su fafata a zagaye na biyu na zaben na shugaban kasa. Al'ummar kasar dai na son ganin lamura sun sauya daga yadda aka saba gani a baya kuma suna son ganin an kawo karshen tsarin nan na dauki dora da shugabanni ke yi sai dai Lionel Zinsou da ke samun goyon bayan shugaba Yayi na ganin al'umma fa ita ce ke da wuka da nama wajen zaben shugaban da zai jagorance su don haka batun dauki dora ma bai taso ba.

A Benin za a yi zagaye na biyu a zaben shugaban kasa
A Benin za a yi zagaye na biyu a zaben shugaban kasaHoto: Getty Images/AFP/P. Ekpei

Su ma dai al'ummar Tsibirin Zanzibar za su kada kuri'a a zagye na biyu, a kasar Kongo kuwa zaben shugaban kasa yayin da al'ummar tsibirin Capeverde kuma za su kada kuri'unsu domin zaben 'yan majalisun dokoki wanda daga haka za su zabi shugaban kasa. A kasar Senigal kuwa zabaen raba gardama za a gudanar duk dai a karshen mako, wato ranar Lahadi 20 ga wannan wata na Maris da muke ciki.