1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin zaben sabon shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka

March 1, 2017

An fatattaki mai horas da 'yan wasan kungiyar Leicester ta Ingila, kana ana shirin zaben sabon shugaban hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Afirka.

https://p.dw.com/p/2YRyq
Afrika Cup Tunesien vs Sambia 22.01.2015
Hoto: K. Desouki/AFP/Getty Images

Mai horas da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Leicester da aka fatattaka daga bakin aiki Claudio Ranieri ya ce mafarkinsa ya kawo karshe. Kuma tuni ya yi sallama da 'yan wasan. Sallamar da aka yi wa Claudio Ranieri ya zo da ba zata ga magoya bayan kungiyar ta Leicester gami da sau8ran masu sharhi kan lamuran wasanni. Matakin ya zo dai dai lokacin da kungiyar take matsayi na uku daga kasa a jerin tebirin gasar lig na Premier da ke gudana a Ingila.

Fußball Leicester City Trainer Claudio Ranieri
Hoto: Getty Images/M. Regan

Shi dai Claudio Ranieri ya yi suna lokacin da babu zato babu tsammani ya jagoranci wannan kungiyar ta Leicester City ta lashe gasar lig na Premier lamarin da ya jijjiga masoya kwallon kafa da masu sharhi a duniya baki daya.

A Ingila a gasar kofin kalubale da aka kara kungiyar Manshester United ta lashe gasar bayan doke Southampton da ci 3 da 2.

A gasar Bundesliga na lig na Jamus da aka kara a karshen mako kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da ta karbi bakuncin kungiyar Hamburg, inda ta yi wa 'yan Hamburg cin kacar tsohon keke, rakacau, na ci 8 da nema yayin wasa na ranar Asabar.

Haka kungiyar Leipzig ta doke Kolon na da ci 3 da 1. Kana Dortmund da bi Freiburg har gida ta doke ta da ci 3 da 0. Yayin da Hertha Berlin ta doke Eintracht Frankfurt da ci 2 da nema.

DFB-Pokal | Eintracht Frankfurt vs DSC Arminia Bielefeld
Hoto: picture-alliance/Pressefoto Rudel

Anata bangaren kungiyar Mainz ta doke Leverkusen da ci 2 da nema. Sannan Augsburg ta doke Darmstadt da ci 2 da 1.

A gasar na Bundesliga da ke gudana a Jamus har yanzu kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ke jagorancin teburin da maki 53, sai Leipzig a matsayi na biyu da maki 48, yayin da Borussia Dortmund take matsayi na uku da maki 40.

A gasar La Liga na Spain kungiyar kwallon kafa Real Madrid ke ci gaba da jagoranci teburin da maki 52, yayin da Sevilla mai mara mata baya ke da maki da maki 52. Kana Barcelona tana matsayi na uku da maki 51.

An bude gasar neman cin kofin kwallon kafa na Afirka na matasa 'yan kasa da shekaru 20 a birnin Lusaka na kasar Zambiya karo na 14. Yayin wasan farko jiya Lahadi mai masaukin baki Zambiya ta samu nasara kan Guinea da ci 1 mai ban haushi.

Schweiz, Ballon d'Or Gala 2015 Issa Hayatou und Lionel Messi
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Sprich

A  yayin da Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka ke shirin gudanar da zaben shugaban hukumar ta CAF ranar 16 ga watan Maris a birnin Adis Ababa na Habasha, wanda kuma shugaba mai ci Isa Hayatou ke son yin ta zarce karo na takwas, alamu sun fara nunawa da kyar ya kai labari, ganin cewa ya yi shekaru 28 yana rike da wannan mukami, kuma an samu canji a hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, sabbin jini sun kunno kai suma suna son canji a Africa domin ci gaban hukumar ta CAF, wanda tuni an fara nuna Shugaban hukumar kwallon kafan Madagascar Ahmed Ahmed wanda ya nuna sha'awar tsayawa da ya fito takarar da karfinsa domin yana da goyon bayan kasashe masu son canji kamar Nigeria, Africa ta Kudu da Zimbabuwe.

Olympia Rio 16 20 08 Momente 5000 Meter Herren Mo Farah
Hoto: Reuters/K. Pfaffenbach

Dan wasan gudu na Olympic na Birtaniya, Mo Farah wanda ya lashe gasar gudun dogon zango na Olympic, ya tabbatar da kare kansa cewa bai taba mu'ammali da kwayoyin masu saka kuzari ba. A cikin wata sanarwa Mo farah ya musanta labarin wata mujallah kan bayanan da aka sata da cikin skaonsa na email da ke nuna mai horas da shi dan Amirka ya ba shi magungunan.

Farah ya bayyana kansa a matsayin dan wasa wanda bai taba karya doka ba game shan kwayoyin kara kuzari, kuma ya yi watsi da duk wani zargi kan haka. Shi dai Farah ya lashe gudun mita 5,000 da 10,000 a sheakra ta 2012 da 2016.