1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

SHIRIN ZABE A KASAR KAMAROU..............

ZAINAB AM ABUBAKAR.

Kasar Kamaru na mai zama daya daga cikin kasashen nahiyar afrika da zaa gudanar da zabe a wannan shekara.Inda mata suka duka kain da nain wajen ganin cewa yar takara a wannan zabe ta cimma nasaran lashe wannan zabe.Eugenie Zambo,itace mataimakiyar shugabar wata kungiya dake campaign din shigar da matan kasar cikin harkokin siyasa,inda tace lokaci yayi da mata zasu fice daga kangin bakin ciki da zulumi da suke ciki domin karawa da takwarorinsdu maza a fannoni daban daban.

Kididdiga da hukumar kidayan jamaa ta janhuriyar kamaru ta gabatar na nuni dacewa akalla kashi 52 daga cikin dari na adadin yawan jamaar kasar million 15 da dubu dari 8 mata ne,abunda ke dada tabbatar dacewa idan har sun shiga harkokin zaben wannan kasa zasu iya rinjayen maza a mukamai da zasuyi takara.

A shekara ta 1960 ne kamaru ta samu yancin kai,daga wannan lokaci ya zuwa yanzu shugabannin kasa biyu kadai akayi a wannan kasa,Ahmadou Ahijo daya mulki kasar daga 1960-1982da shugaba Poul Biya wanda ke mulkin kamaru daga shekara ta 1982 zuwa yanzu.A shekarata 1975 ne aka nada mace ta farko zuwa mukamin miniasta.A halin yanzu kuwa akwai mata ministoci biyu,Catherine Bakang Mbock mai kula da harkokin mata,da Cecile Bomba Nkolo dake lura da maaikatar raya jindadi.

Wata wakiliyar kungiyar fafutukan ilimi wa mata a Kamarou Claire Eza,tace lokaci yayi da jammiiyun siyasa zasu daina nunawa mata wariya,inda ta kara dacewa daga yanzu zuwa watan Oktober kungiyoyi masu zaman kansu na mata zasu taka rawar gani wajen ilimantar dasu muhimmancin fitowa domin kwatan yancinsu daga Maza.To sai dai ba dukkan matan kasar ne suka amince dacewa lokaci yayi da mace zata riki kujeran shugabanci ba,ballan tana kasancewa a fadar gwamnati da ake kira Etoudi.A ta bakin shugabar shirin yaki da talauci Jeane Teumo,da sauran rina a kaba dangane da shigar mace mukamin shugabancin Kamaru,amai makon haka injita,abunda yafi muhimmanci wa matan shine samun ilimitare da yakan talauci.Ta bada misalin cewa ,kungiyoyi dake ikirarin kamfain wa zaban mace a matsayin shugabar kasa sun kasa cimma daidaituwa kann tsari guda,domin dukkaninsu na kokarin samarda kudade ne domin biyan bukatun kungiyoyin nasu.Ita kuwa Grace Ebelle cewa tayi mafarki kadai wadannan kungiyoyi keyi.Tace idan sun hadu a taro banda hararan juna babu abunda matan keyi,tayaya zasu cimma burinsu na zaban mace guda?wannan batu ne injita na fira kawai tsakanin matan.

Shi kuwa mai bada shawara kann harkokin fasaha na maaikatar ayyuka Benard momo cewa yayi,yana da kyau kaga mata suna fafutukan abunda suka kira yancinsu,to sai dai ba a irin tarurruka dake karewa baran baran ,zai kasance abu mawuci su cimma wani tudun dafawa.