Shirin zaɓen shugaban ƙasa a Abiru Kwas | Labarai | DW | 05.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin zaɓen shugaban ƙasa a Abiru Kwas

Hukumomi a ƙasar Abiru Kwas sun sanar da cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a ranar 31 ga watan oktoba mai zuwa

default

t Laurent Gbagbo

Firaministan ƙasar Abiru Kwas Gillaume Soro ya sanar da cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a ranar 31 ga watan Oktoba mai zuwa. Hukumar zaɓe dai ta ƙasar ita ce ta gabatar da shawara ga gwmnatin domin tsaida ranar zaɓen, wanda aka saka ranar tun can da farko shekaru biyar da suka gabata.

Tun a shekara ta 2005 ne dai ake famar kai ruwa-rana kan maganar zaɓen saboda rashin fahimtar juna da aka samu tsakanin 'yan siyasar ƙasar dangane da batun yin rejista.

Masu aiko da rahotannin sun ce har yanzu dai ba a da tabas dangane da shirya  zaɓen saboda rikicin da ake ci-gaba da samu tsakanin shugaba Laurent Gbagbo da kuma sauran 'yan siyasar ƙasar

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita       : Ahmad Tijani  Lawal