Shirin zaɓen raba gardama a kudancin Sudan | Labarai | DW | 24.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin zaɓen raba gardama a kudancin Sudan

Taron Majalisar Ɗinkin Duniya ya bada goyan baya ga zaɓen raba gardama a kudancin Sudan

default

Salva Kiir da Omar Hassan el Beshir na tattanawa

A yayin da a ke gudanar da taron babban zauren majalisar duniya, a na sa ran cewa shugabani a taron  zasu tattauna fargaban ɓarkewar yaki a Sudan da kuma yiwuwar ɓallewar ƙasar, shekaru biyar bayan da a ka kammala yarjejeniyar samar da zaman lafiya a ƙasar wadda ta kawo ƙarshen yaƙin basasa. Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta ce ƙasar Sudan a halin yanzu tamkar ɗannanen bam ne da ke jira ya fashe. Za'a gudanar da zaɓen raba gardamar da zai ba kudancin ƙasar wadda take da arzikin man fetur 'yancin kanta a ranar tara ga watan Janairun baɗi. Har yanzu ana ƙoƙarin jinkirta shirye-shiryen amma ana tsoron cewa yin hakan zai jagoranci 'yan tawayen da ke kudancin ƙasar su ɓalle.

Wani jami'i daga ma'aikatar kula da harkokin cikin gidan Amurka ya ce maƙusudin taron yau Juma'a a zauren majalisar, shine a bai wa arewaci da kudancin Sudan ƙarfin gwuiwa domin su haɗa kai su yi aiki tare.

Shugaban ƙasar Kenya Mwai Kibaki ya ce ya sami tabbacin daga shugaban kudancin Sudan Salva Kiir da shugaba Omar al-Bashir cewar za a gudanar da ƙuri'ar raba gardamar a kudancin Sudan kamar yadda a ka shirya.

Mawallafi: Pinaɗo Abdu

Edita: Ahmed Tijani Lawal