Shirin zaɓe a Guinea na fuskantar Ƙalubale
October 22, 2010Sabon shugaban hukumar zaɓe a ƙasar Guinea, ya yi gargaɗin cewa har yanzu babu wani shiri takamaimai da aka yi, domin gudanar da zaɓen ƙasar a ran lahadi mai zuwa kamar yadda aka tsara, wanda kuma ake sa ran zai mayar da ƙasar bisa turbar demokraɗiyya. Siaka Toumany Sankare, wanda aka naɗa, a matsayin shugaban hukumar zaɓe a ran talata, bayan da aka zargi tsohon shugaban da murɗiyya, ya ce zai yanke shawarar ko za'a yi zaɓen a yau Juma'a. A halin da ake ciki yanzu, ministan harkokin wajen Faransa Bernard Kouchner ya bada shawarar a jinkirta zaɓen. Wannan zagaye na biyu na zaɓen dai za'a fafata ne tsakanin Cellou Dallein Diallo tsohon Frimiyar ƙasar da shugaban 'yan adawar ƙasar Alpha Conde.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Umaru Aliyu