1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin yiwa tsarin kiwon lafiyar Amirka garambawul

Majalisar wakilan Amirka na kan kaɗa ƙuri´a kan yiwa tsarin kiwon lafiyar ƙasar gyaran fuska

default

Shugaban Amirka Barak Obama

Majalisar wakilan Amirka na shirin kaɗa ƙuri´a akan shirin shugaba Barak Obama na yiwa tsarin kiwon lafiyar ƙasar kwaskwarima, shirin da ake taƙaddama kansa. Bayan ya shafe sama da shekara guda yana ƙoƙarin shawo kan ´yan jam´iyar adawa ta Republicans, shugaba Obama na fatan samun ƙuri´u 216 da yake buƙata don zartas da wannan mataki da ake kace-nace kansa. Ko da yake ana sa rai ƙuri´ar za ta yi ƙarfi, amma an jiyo Obama na mai kyautata fatan cewa sabon tsarin zai samu amincewar ´yan majalisar. A lokacin da yake jawabi ga ´yan majalisar Obama cewa yayi.

"Ba ni za ku yiwa ba. Ba jam´iyar democrats za ku yiwa ba. A´a ku yiwa al´umar Amirka domin su ne ke son ganin an ɗauki wannan gagarumin matakin."

To sai dai a lokaci ɗaya shugaban ya amsa cewar gyarar fuskar da za a yi wa tsarin kiwon lafiya ba zai iya magance dukkan matsalolin da ke a ƙasa ba.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala