1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin yafewa kasashe matalauta bashi ya fara aiki

A yau hukumar bayarda lamuni ta duniya ta sanar cewa daga jiya alhamis shirin yafewa kasashe mafiya talauci a duniya 19 basusuka dake kansu ya fara aiki.

Kakakin hukumar yace yafe bashin, karkashin wani shiri na kasashe 8 masu arzikin masanaantu ya fara aiki wanda hakan ya nuna bashin ya tafi nan take daga kann kasashen da aka amince zaa basu wannan sauki.

A ranar 21 ga watan disamba daya gabata ne hukumar gudanarwa ta IMF ta amince yafe bashin dala biliyan 3 da digo 3 da ake bin kasashe matalauta da suka hada wasu kasashen nahiyar Afrika guda 12,ciki kuwa har da Ghana Nijar Burkina Faso da Senegal da Mali.