Shirin Unicef akan yara da mata a Nigeria | Labarai | DW | 21.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin Unicef akan yara da mata a Nigeria

Asusun tallafawa yara na Mdd, wato Unicef a takaice ,ya kaddamar da wani shiri na tantance yanayin da yara kana na da kuma mata ke ciki a Nigeria.

Shirin , wanda ke samun tallafin hukumar kididdiga ta kasa, an shaidar da cewa tuni ya fara tattara bayanai daban daban, dake da nasaba da yara da kuma mata a fadin kasar baki daya.

Wasu daga cikin fannin da wannan aiki ya shafa , sun hadar da mace macen yara sakamakon rashin abinci mai gina jiki da kuma rashin kyakkyawan ruwan sha.

Rahotanni dai sun nunar da cewa hukumomi biyun na gudanar da wannan shirin ne, da nufin inganta rayuwar kana nan yaran ne da kuma mata a kasar ta Nigeria.

Ya zuwa yanzu dai hukumar ta Unicef ta kashe a kalla dala miliyan 1 da digo 5, wajen gudanar da shirye shiryen inganta rayuwar yara da kuma mata a kasar.