Shirin tsagaita wuta tsakanin Isra´ila da Falasdinawa na fuskantar kalubale | Labarai | DW | 26.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin tsagaita wuta tsakanin Isra´ila da Falasdinawa na fuskantar kalubale

Mukaddashin shugaban Hamas dake gudun hijira a Damascus babban birnin kasar Syria, Musa Abu Marzuk ya ce kungiyarsa a shirye ta ke ta tsagaita wuta da Isra´ila amma sai kasar ta Bani Yahudu ta daina cin zalin Falasdinawa. Wadannan kalaman na Abu Marzuk sun zo ne a daidai lokacin da Isra´ila ta janye dakarunta daga Zirin Gaza yau da safe yayin da wani shirin tsagaita wuta ya fara aiki nan take da zumar kawo karshen munanan artabun da aka shafe watanni 5 ana yi. To amma Hamas da kungiyar Jihadin Islami sun harba rokoki cikin Isra´ila suna masu cwea ba su da niyar daina kai hare hare.

Firaministan Isra´ila Ehud Olmert ya umarci sojojinsa da su nuna juriya. Shi kuwa mataimakinsa Shimon Peres ya bayyana manufar shirin tsagaita wutar ce yana mai cewa.

“Bangaren Falasdinawa ya fahimci cewar babu zabi da ya kai kawo karshen yaki kuma a fara tattaunawa. Ina jin Abu Mazin ya taka muhimmiyar rawa bisa manufa saboda haka muna gode masa. Matsalolin da ake fuskanta yanzu ba zasu canza komai ba. Dukkkan mu ba mu da wani zabi da ya fi zaman lafiya.”