1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Shirin taimakawa masu watsi da tsattsauran ra´ayin addini

Tun a cikin watan Afrilun shekarar 2008 aka kafa gidauniyar Quilliam a birnin London inda tsaffin masu matsanancin ra´ayin addinin Musulunci ke taimakawa don yaƙi da tsauttsauran ra´ayi a cikin addinin

default

Tambarin gidauniyar Quilliam, dake yaƙi da matsanancin ra´ayin addinin Musulunci

Kasancewa masu wannan namijin aiki a yanzu sun san irin kalamai na yaudara da hanyoyin da ake amfani da su wajen shawo kan matasa su rungumi tsattsauran ra´ayin addini, ya sa sun ɓullo da na su dubarun domin kuɓutar da matasan daga hannun masu amfani da addini don biya wasu bukatu na su.

Tun a cikin watan Afrilun shekara ta 2008 wannan gidauniya ta Quilliam Foundation ta kafu a birnin London na ƙasar Birtaniya. An ba ta wannan suna ne don nuna girmamawa ga Sheikh William Henry Abdullah Quilliam, wani Baturen Ingila da ya musulunta tun a farkon ƙarni na 20, kuma mutumin da ya gina masallaci na farko a Ingila. Wannan gidauniya ko kuma ƙungiya tana bawa musulmai shawarwari musamman waɗanda ke neman hanyar fita daga bin ƙungiyoyi na masu matsanancin ra´ayin addinin Musulunci. A halin da ake ciki gidauniyar ta Quilliam tana da zaunannun membobi 15 dukkansu tsoffin masu matsanancin ra´ayin addinin na Musulunci. Ɗaya daga cikinsu shi ne Ishtiaq Hussain wanda iyayensa suka yi ƙaura daga ƙasar Pakistan zuwa Birtaniya. Yayi bayani game da halin da ya kasance ciki lokacin yana cikin wata ƙungiyar masu matsanancin ra´ayi.

“Tun a lokacin da nake cikin wannan ƙungiya na sha tababa akan abubuwa da dama da nake ganin ba su dace ba. To amma na yi ta ƙoƙarin yin watsi da su. Kamar kana cikin wata soyayya ce, wasu lokutan za ka ga wasu abubuwa masu takaici da ba su dace, amma saboda soyayya, kamar yadda masu iya magana kan ce ne wai hana ganin laifi, sai ka kawad da kai daga waɗannan abubuwan da ba su dace ba. Amma da zarar soyayya ta ƙare sannan za ka gane kura-kuran da ka yi. Hakan ya kasance da wannan ƙungiya, sai bayan na fice daga cikinta sannan na fara ganin abubuwan da suke yi ba daidai ba ne.”

Shi dai Ishtiaq Hussain tsohon mai ra´ayin riƙaun addinin Musulunci ne. Yana da shekaru 30, a Birtaniya aka haifeshi kuma a can ya girma. Iyayensa sun fito ne daga ƙasar Paskistan. Ya shafe shekaru takwas a cikin ƙungiyar Hisbut-Tahir ɗaya daga cikin ƙungiyoyin masu matsanancin ra´ayin addinin Musulunci dake gwagwarmayar wanzar da shari´ar Musulunci a faɗin duniya. A nan Jamus an haramta ayyukan wannan ƙungiya saboda manufarta ta ƙyamar Yahudawa. Ƙungiyar ta Hisbut-Tahir ta kasance tamkar mafaka ta mu´amala da addini ga Ishtiaq Hussain. Ya sha da ƙyar a ƙoƙarinsa na ficewa daga wannan ƙungiya. Ishtiaq ya kasance cikin rashin sani yayin da ƙungiyar ke ƙara matsa masa lamba.

“Sun fara gaya min cewa shaiɗan ne ke saka waswasi da shakku cikin zuciya ta akan abin da na sa gaba. Suka ce bai kamata in faɗa cikin tarkon shaiɗan ba. Ya zama wajibi in tsaya kai da fata akan abin da na yi imani wato in bari imani na ya yi ƙarfi. Amma na nema gare su da su yi mini bayani me ya sa a cikin al-Qur´ani ba a wajabta mana kafa wata ƙasa me bin shari´ar musulunci tsantsa ba? Mai ya sa a cikin al-Qur´ani ba a ce addinin Musulunci wata aƙidar siyasa ba ce? Me yasa a cikin littafin mai tsarki aka ce Musulunci addini ne kaɗai? To amma wallahi sun kasa ba ni amsoshin waɗannan tambayoyi.”

Ishtiaq Hussain dai ya tashi ne a wani gida mai mutunci. Ya samu tarbiya ta gari sannan abokansa kuma duka mutane na gari. To sai dai duk da haka ba ya jin kansa a matsayin cikakken ɗan Birtaniya yayin da a Pakistan kuma yake zaman baƙo. Bai samu taimakon da yake so ba daga limaman masallacin unguwarsu domin limamin ya fito ne daga wata al´ada daban sannan bai iya turanci sosai ba.

“A matsayin ka na matashi da ba wanda zai ce yi ko kar ka yi, ba ka jin wata dangantakarka da masallaci, domin babu wani abu da za ka samu a can kasancewar duk huɗuba da wa´azin da ake yi, a cikin wani harshe da ba ka iya ba. Matashi a wannan ƙasa dake son neman fahimtar addininsa ba zai samu a masallaci ba, domin limaman na magana ne a cikin wani harshe daban. Kamar ni ga misali, iyaye na ba sa sha´awar batutuwa na addini da siyasa, saboda da haka cikin sauƙi kana iya karkata ga wasu mutane da za su saurare ka da nufin share maka hawaye. Irin waɗannan ka iya zama ƙungiyoyi masu matsanancin ra´ayi.”

A dai halin da ake ciki masallatai da yawa sun ƙara buɗe ƙofofinsu ga matasa dake neman ƙarin sanin addinin Musulunci. Ita ma ƙungiyar Hisbut-Tahir ta fara nuna sassaucin aƙida, amma har yanzu ta na bin manufofinta na da. Kana kuma ba abin da ya canza a tsarinta na ɗaukar sabbin membobi, inda suke farawa da wata tambaya mai sauƙi.

“Su kan tambaye ka ko kai wane ne? Yaya za ka iya bayanin asalinka? Idan ka ce kai ɗan Birtaniya ne ko Pakistan, sai su ce a´a ba haka ba ne kai ba ɗan Birtaniya ba ne ko Pakistan ko Balarabe ko ɗan Afirka. Domin a gare su nuna asali na ɗan wata ƙasa, ra´ayi ne na ´yan mulkin mallaka da suka cusa mana cikin zukatanmu amma Mahaliccinmu ba. Dole ne ka ɗauki kanka a matsayin Musulmi sannan kuma ga ´yan´uwanka Musulamai ne kaɗai zaka iya biyayya amma ba ga wa´yansu daban ba.”

Bayan haka sai a fara wata tattaunawa mai sarƙaƙiya domin cusawa sabbin membobi ra´ayin ƙyamar waɗanba ba Musulmi ba. Ga Ishtiaq Hussain an fara wanke masa ƙwaƙwalwa ne da kisan ƙare dangi da aka yi a Bosniya wasu kuwa akan shawo kansu ne da yaƙe-yaƙen Afghanistan da Iraqi. Da zarar ka zama memba a ƙungiyar ta Hisbut-Tahir sai a tayar da batun kafa wata ƙasar Musulunci a duniya baki ɗaya. Saboda haka ya zama wajibi a yaƙi ƙasashen da ba na Musulmai ba. Bayan ya zama memba, Ishtiaq ya yi tafiye tafiye zuwa ƙasashe da dama domin samawa ƙungiyar sabbin membobi. To sai dai a nan ya haɗu kuma da masana addinin Musulunci waɗanda suka yi fatali da manufofinsa bisa hujjoji daga al´Qur´ani mai tsarki. A ƙarshe shi da kansa ya nuna shakkunsa a fili.

“Shin a ina cikin al-Qur´ani aka umarce mu da mu kashe mutane da ba su ji ba su gani ba, ciki har da musulmai da sunan jihadi? Shin wa zai amince da wannan a matsayin manufar wani addini?”

Hatta su kansu masu matsanancin ra´ayin sun ka sa ba shi amsa. A dangane da haka Ishtiaq ya gano cewa ana amfani da addinin Musuluncin don yaɗa aƙidoji na siyasa. Yanzu haka dai yana aiki ne da gidauniyar Quilliam wadda ta ƙunshi tsoffin masu tsattsauran ra´ayin addini amma yanzu suke bin wasu dubaru na yaƙi da matsancin ra´ayin Musulunci. Ishtiaq yana bawa ´yan sanda da jami´an tsaro shawara, yana zuwa makarantu da jami´o´i don wayarwa da matasa kai. Kana kuma yana shiga cikin muhawwarori musamman na ƙungiyoyin Musulmai.

“Manufar wannan ƙungiya kenan ta Hisbut-Tahir da ma sauran ire irensu kamar su al-Qaida. Saboda haka alhaki ne da ya rataya kan Musulman ƙwarai da su yaƙi wannan mummunar aƙida da ake yaɗawa da sunan Musulunci. Ya kamata Limamai da sauran Malamai masana addinin Islama su haɗa kai su faɗakar da jama´a cewa tsattsauran ra´ayi bai da tushe a cikin Musulunci. Da yawa daga cikin masu kafa irin waɗannan ƙungiyoyi masu matsanancin ra´ayi ba malaman addinin Musulunci, likitoci ne da lauyoyi da kuma injiniyoyi.”

To sai dai Ishtiaq Hussain na mai ra´ayin cewa haramta irin waɗannan ƙungiyoyi kuskure ne, domin hakan zai sa su riƙa tafiyar da aikinsu a ɓoye. Ya ce a gidauniyar Quilliam sun yi imanin cewa ta tattaunawa da muhawwarori masu ma´ana sune hanyoyin mafi dacewa wajen canza ra´ayoyin waɗannan mutane.

Mawallafa: Ruth Rach/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Ahmed Mohammed

Sauti da bidiyo akan labarin