Shirin sake zabe n shugaban kasa a Chile,yayinda mace ta tashi lashewa
December 12, 2005Talla
An shirya sake gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Chile,yayinda yar takara Michelle Bachelet ke kan gaba a zaben jiya lahadi.
Ita dai Michelle wadda aka taba daurewa a gidan yari a lokacin mulkin sojin kasar ,wadda daga bisani kuma ta rike mukamin ministar tsaro ta kasar,ta samu kashi 45 da digo 8 bisa dari na kuriu kashi 96 da aka kirga a yanzu,amma sai dai bata samu fiye da kashi 60 cikin dari da ake bukata ba, da zai bata damar zama mace ta farko shugabar kasar.
Wanda ke bi mata a yawan kuriu wanda zasu sake fafatawa a zagaye na biyu na zaben,dan kasuwa Pinera yana da kashi 25 da digo 4 na kuriun da aka kidaya.
A ranar 15 ga watan janairu mai zuwa ne dai zaa sake gudanar da zaben.