A cikin shirin bayan labarun duniya akwai rahotanni da suka hada da ziyarar da 'yar takarar jam'iyyar masu kyamar baki ta Faransa Marine Le Pen ta kai Chadi. A Najeriya ana mayar da martani dangane da gabatar da mutane 20 da rundunar ‘yan sandan kasar ta yi wadanda ake zargi da laifin kashe-kashe a garin Ile Ife.