shirin Najeriya na aikewa da dakarunta Somalia | Labarai | DW | 24.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

shirin Najeriya na aikewa da dakarunta Somalia

Cikin makonni biyu masu zuwa ne ake sa ran dakarun Najeriya zasu tashi zuwa kasar Somalia a matsayin wani bangare na dakarun AU.

Ministan tsaro na Najeriya Thomas Aguiyi Ironsi ya fadawa kanfanin dillancin labaru na reuters cewa tuni bataliyar najeriyar wadda ke dauke da sojoji 770 zuwa 1000,da zata Somalia ta shiga aka fara horas dasu inda yanzu haka suke dakon kayan aiki kafin su kama hanyarsu ta zuwa kasar ta Somalia.

AU dai tun farko ta shirya aikewa da dakarun ta 8,000 izuwa Somalia.

Komitin sulhu na MDD ya goyi bayan gagauta aikewad da wadannan dakaru zuwa kasar da ba ta samu zaman lafiya ba a 15 dasuka shige.