1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin mayar da 'yan gudun hijrar Myanmar

Ramatu Garba Baba
September 19, 2017

Shugabar Myanmar Aung San Suu Kyi a wannan Talatar ta sanar cewa gwamnatin kasar ta tsara shiri na musanman don soma maido da 'yan kasar da ke gudun hijra.

https://p.dw.com/p/2kF8f
Bangladesch Rohingyas im Flüchtlingslager Cox's Bazar
Hoto: Reuters/M.P. Hossain

Suu Kyi ta ce a shirye gwamnati ta ke ta dawo da dubban 'yan kabilar Rohingya da suka tserewa rikici zuwa Bangladesh da ke makwabtaka da kasar in har sun amince su dawo kasar. Shugabar ta fuskanci matsin lamba daga kasashen duniya kan matakinta na kin kare 'yan kabilar Rohingya a rikicin da ya barke a watan da ya gabata inda aka kona kauyukan da musulmin ke zaune, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da kuma tilastwa dubban mutane tserewa daga kasar. A halin da ake ciki, Suu Kyi ta mika goron gayyata ga wakilan kasashen duniya na ziyartar jahar Rakhine don gane wa idanunsu zarge-zargen da ake yi wa gwamnatinsu na kokarin shafe al'ummar Rohingya daga doron kasa. Aung San Suu Kyi ta musanta duk wadannan zarge-zargen.