Shirin kidaya a Nigeria | Labarai | DW | 16.03.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin kidaya a Nigeria

Rahotanni daga tarayyar Nigeria na nuni dacewa an kammala horar da jamian gudanar da kidayar jama da zaa gudanar a mako mai zuwa a wannan kasa dake da mafi yawan alumma a nahiyar Afrika.

Bugu da kari an fara shirya gabatarwa jamian aikin takardun da zaa cike alokacin wannan kidaya.

Manajan hukumar kidaya ta kasa Dr Ismail Suleiman ya bayyana cewa jamian zasu fara sanyawa gidaje lambobi nan bada jimawa.

Kasancewar shirin kidayar jamaan na fuskantar matsaloli a mafi yawan jihohin kasar ,Dr Suleiman yayi karin haske dangane irin matakai da suka dauka.

Adangane batu na rashin amincewa maza su shiga gidajen kulle domin gudanar da aikin kidayan kuwa,managan shirin yace sun sanya mace acikin kowane ayarin jamiai,wadanda zasu iya shiga gidajen da maza basa shiga a ayayin kidayan.Ranar talata nedai ake saran fara kidayar alummar ta Nigeria,shirinda zai dauki kwanaki 5 yana gudana.

 • Kwanan wata 16.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7M
 • Kwanan wata 16.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7M