Shirin karbar sabbin kasashe a Kungiyar Tarayyar Turai | Siyasa | DW | 22.04.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirin karbar sabbin kasashe a Kungiyar Tarayyar Turai

A ranar daya ga watan mayu mai zuwa ne za a kaddamar da bikin karbar sabbin kasashe goma a Kungiyar Tarayyar Turai dake da shekwatarta a birnin Brussels

Bikin kammala shirye-shiryen shiga KTT a Riga, babban birnin Latviya

Bikin kammala shirye-shiryen shiga KTT a Riga, babban birnin Latviya

Ko shakka babu a game da cewar mutumin da zai fi kowa doki da murna a shagulgulan da za a gabatar game da karbar kasashe kamarsu Malta da Cyprus a kungiyar tarayyar Turai (KTT) a ranar daya ga watan mayu mai zuwa shi ne Günter Verheugen, kantomar hukumar zartaswa ta kungiyar akan al’amuran karbar karin kasashe karkashin tutarta. Jami’in siyasar ya taka muhimmiyar rawa wajen hada kan matakan karbar sabbin kasashen a cikin shekaru biyar da suka wuce. Ranar ta daya ga watan mayu, rana ce ta tarihi a gare shi, kamar yadda ya nunar, ya kuma kara da cewar:

Wannan ci gaba na ma’ana ne cewar tuni wannan bangare na Turai da lamarin ya shafa ya warke daga tabon da ya biyo bayan ta’asar mulkin ‚yan Nazi da kuma yakin duniya na biyu. A yanzu za a shiga wani sabon babi na zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsaro da kuma yalwa tsakanin kasashen East Sea da na Bahar Aswad.

Dukkan kafofin kungiyar ta tarayyar Turai dake Brussels suna da cikakken shiri na tafiyar da al’amuran kungiyar da zata wayi gari tana kunshe da mutane miliyan 455 karkashin tutarta. An dai fuskanci wahala wajen daidaita al’amuran tsaffin kasashen kwaminis guda takwas domin cimma matsayin da ya dace na shigowa inuwar kungiyar. Amma ala-kulli-halin kwalliya ta mayar da kudin sabulu dangane da wannan manufa a cewar Verheugen. Kasashen sun yi namijin kokari wajen aiwatar da garambawul da ya dace ga manufofinsu na siyasa da tattalin arziki da kuma zamantakewar jama’a ta yadda, duk da wasu ‚yan matsaloli da za a iya fuskanta nan gaba, amma karbar tasu ba zata hana ruwa gudu ga ayyukan Kungiyar ta Tarayyar Turai ba. Bisa ga ra’ayin Verheugen mai alhakin jan akalar matakan karbar sabbin kasashen matsalar dake akwai shi ne kasancewar al’umomin wadannan kasashe ba su da wata cikakkiyar masaniya a game da kungiyar. To sai dai kuma wannan tsofuwar matsala ce da ta shafi har da tsaffin kasashenta. A dai halin yanzu haka hukumar zartaswa ta KTT na da niyyar gabatar da shawarwarin karbar kasar Krowashiya, a yayinda ake sa ran samun wata takamaimiyar shawara daga kantoman hukumar akan karbar sabbin kasashe Günter Verheugen akan kasar Turkiyya, wacce ake fama da sabani kanta, nan da watan satumba mai zuwa. A cikin wani bayani da yayi Verheugen karawa yayi da cewar:

A hakikanin gaskiya, maganar Turkiyya abu ne dake da sarkakiyar gaske, saboda matsala ce dake da muhimmanci a siyasar duniya baki daya. Maganar ta shafi makomar Turkiyyar ce a nahiyar Turai da kasashen yammaci. Lamari ne dake da tasiri akan dangantakar kasashen yammaci da na duniyar Musulmi.

Bisa ga ra’ayin Verheugen ko da yake Turkiyya na samun ci gaba, amma tana fama da wahala wajen aiwatar da garambawul ga manufofinta. Ita dai gwamnati a fadar mulki ta Berlin tana goyan bayan karbar Turkiyya, a yayinda Faransa ta fara bayyana kyamar hakan baya-bayan nan.