shirin kafa cibiyar cafke makamai a turai | Labarai | DW | 11.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

shirin kafa cibiyar cafke makamai a turai

Shugaba Bush na Amurka ya isa babban birnin kasar Bulgaria wato Sofia. Tattaunawar Mr Bush da shugabannin na Bulgaria, zata mayar da hankali ne kann, shirin Amurka na kafa cibiyar cafke makamai masu linzami ne a nahiyar Turai. Bugu da kari, shugaban na Amurka zai kuma tattauna batun makomar kasar sarbiya da mahukuntan na Bulgaria. Kafin dai isar Mr Bush birnin na Sofia, ya kai wata yar karamar ziyara izuwa kasar Albania.Jim kadan da ganawar sa da Faraminista Sali Berisha na kasar, Mr Bush ya jaddada muhimmancin shirin Mdd na tabbatarwa Kosovo cikakken yanci. Da yawa dai daga cikin mazauna Kosovo, yan kabilar albaniyawa ne. Tuni dai kasar Sabiya da kuma Russia suka hau kujerar naki a game da wannan shiri na Mdd. Rahotanni dai sun nunar da cewa, Kasar ta Bulgaria na matsayin zangon karshe na ziyarar da Mr Bush keyi ne, a nahiyar turai.