1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin horas likitocin mata da yara a Afirka ta Yamma

Gazali Abdou Tasawa
April 17, 2018

Hukumar Lafiya ta Afirka ta Yamma ta sanar da shirin bayar da horo ga wasu likitocin 250 na wasu kasashen Afirka guda shida da ke fuskantar kalubale a fannin kiwon lafiyar uwa da danta.

https://p.dw.com/p/2wDWF
Kenia Kenyatta National Hospital - Krankenhaus in Nairobi
Hoto: picture-alliance/dpa/Kenyatta National Hospital

Hukumar Lafiya ta Afirka ta Yamma wato OOAS ta sanar da shirin bayar da horo a karo na farko ga wasu likitocin 250 na wasu kasashen Afirka guda shida da ke fuskantar kalubale a fannin kiwon lafiyar uwa da danta wannan kuwa domin yaki da matsalar mace-macen yara kanana a kasashen.

Jean Jacques Kablan shugaban hukumar ta OOAS ne ya sanar da hakan a wannan Talata inda ya ce shirin zai shafi likitoci 244  na yara da na mata daga kasashen Burkina Faso, Cote d'Ivoire, Mali,Moritaniya Nijar da Tchadi. 

Shirin bayar da horon wanda zai dauki tsawon shekaru biyu zai soma ne a karshen wanann shekara ta 2018. Hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Lafiya ta Afirka ta Yamma ta OOAS da kuma kasashen da za su ci moriyar shirin ne za su dauki nauyin bayar da horon wanda zai gudana a biranen Abidjan da Yamai da kuma Bamako.