Shirin hari a Sudiyya. | Labarai | DW | 23.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin hari a Sudiyya.

Ma’aikatar cikin gida ta Saudiya, tace jami’an tsaron kasar sun kame wasu ‘yan ta’adda, cikinsu da wani bako da yayi shirin kai hare-hare a wasu sanssanoni na kasar. Kawo yanzu dai babu tabbacin cewar ko wannan matakin na da alaka da wani shiri na ƙungiyar al’Qaida na kai hari kan maniyata a birnin Makka. A wata sanarwa da ta bayar, ma’aikatar, ta sanar da kame wasu membobin al-Qaida su 14 tun farkon watan disamba. Kana, rahotanni sunce ranar juma’a da ta gabata ma, sai da jami’ai suka rushe wani shiri na kai hari kan mahajjata da wata kungiya da ke da alaka da ƙungiyar al-Qaida ta yi.