Shinzo Abe ya shiga kwana na biyu na ziyararsa a Amirka | Labarai | DW | 13.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shinzo Abe ya shiga kwana na biyu na ziyararsa a Amirka

Firaministan kasar Japan Shinzo Abe ya shiga rana ta biyu a ziyarar da ya kai a kasar Amirka, inda ya gana da Shuga Donald Trump a fadarsa ta White House kafin daga bisani su tashi zuwa jihar Florida.

USA Besuch Shinzo Abe bei Trump in Washington (Reuters/J. Bourg)

Firaministan Japan Shinzo Abe da shugaban Amirka Donald Trump.

Shugabannin biyu sun yaba dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, inda a rana ta farko suka yi abincin dare tare da iyalansu a fadar shugaban na Amirka, kafin daga bisani su tashi zuwa jihar Florida inda makeken gidan nan na Trump ya ke domin ci gaba da tattaunawa, har ma su dan taba wasan kwallon golf. Firaministan na Japan Abe, na fatan amfani da wannan dama domin tattaunawa da shugaban na Amirka kan halin da duniya ke ciki, da kuma makomar yankunansu inda yake cewa:

"Kasar Japan za ta iya nuna kwarewar da take da ita a fannoni daban-daban domin samar da ci-gaban da Shugaba Donald Trump ke bukata a kasarsa, tare da samar da guraben ayyukan yi ga jama'a, kuma dukanninmu biyu mun amince da tattaunawa tsakanin mataimakina Taro Aso da kuma mataimakin Shugaban Amirka Mike Pense ta yadda za a zurfafa tunanin wajen inganta hulda ta kasuwanci tsakanin kasashen biyu.