1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shinzo Abe ya gana da Donald Trump

Firaministan Japan Shinzo Abe ya zama jagoran wata kasa na farko da ya gana da zababben shugaban Amirka Donald Trump.

Wannan ganawa ta biyo bayan irin kalaman da Mr Trump ya yi amfani da su lokacin yakin neman zabe da ake ganin akwai yuwuwar Amirka ta janye dakaru a kasashen da take da hulda ta kut-da-kut kamar Japan.

Bayan ganawar ta sa'a guda da rabi tsakanin shugaban mai jiran gado na Amirka Donald Trump, da Firaminista Shinzo Abe na Japan, a birnin New York, babu cikakkun bayanai kan batutuwa da mutanen biyu suka tattauna a kai.