1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin wace halitta ake kira spirulina

Bashir, AbbaJuly 21, 2008

Taƙaitaccen bayanin halittar spirulina da abin mamakin da take da shi

https://p.dw.com/p/EgOb
Kududdufin kiwon spirulina a ƙasar SinHoto: AP

Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Abdu Uban-Dawaki daga jihar Kano a Tarayyar Najeriya. Ya ce; Don Allah ina so ku yi min cikakken bayani dangane da halittar nan da ake samu a cikin ruwa, wato Hallitar Spirulina: shin wane irin abin mamaki take da shi kuma yaya ake kiwon ta?

To Spirulina dai wani ƙwaro ne mai kama da gamsakuka da ake samunsa a kududdufai da rafuka, kuma wannan suna Spirulina dai Turanci ne, kasancewar ba mu da sunan wannan ƙwaro da Hausa. Wato abin mamakin shi ne, bisa al'ada, hallittu masu kama da gamsakuka da ake samu a kududdufai da rafuka da tafkuna da magudanan ruwa, suna nuna gurɓata yankin ne da lahanta shi. Amma abin ba haka yake ba ga Spiriluna, domin kuwa a sassan duniya da dama, irin wanan hallita kan fito har a gefen gidaje, kuma ta kan zama abin da ake maraba da ita ga mutanen da ba su da kuzari. Ana iya dafa spiriluna ta bushe tana ƙamshi kamar na busasshen kifi, sai dai hakan ya kan canja idan an haɗa ta da abinci, in da kalarta kan sauya kalar abincin.

Ƙwaron Spiriluna dai, ƙwaro ne da ake ci a duk duniya a matsayin abinci mai gina jiki. Kuma Mujallar kimiyya da aka wallafa ta bayyana spiriluna a matsayin wata babbar hanyar samun abinci mai gina jiki da mutum ya samu. Kusan dukanin jikinsa na ƙunshe da abubuwa masu gina jiki musamman sinadarin amino. Sannan yana da sinadarin vitamin na A da B12 da E, kana ga shi da magunguna da ke kare kamuwa da cututtukan da ke kama fatar jiki, da maganin cutar karairayewar jini watau (Anaemia) da sauran cututtukan zuciya da na jijiyoyi.

To albishir mai daɗi ga iyaye mata shi ne, an gano cewar wannan halitta ta taimaka kuma har yanzu tana kan taimakawa wajen shayar da yaran da basu da ƙarfin garkuwar jiki a Indiya da Afrika. A jamhuriyar Dimmukaradiyar Kongo akwai gonakin da ake kiwon spiriluna da
kuma ƙasashen jamhuriyar Benin, Chadi, Indiya, China, Japan da Mexico.

Ana iya kiwon sprilina a kududufin ruwa mai faɗin sikwaya mita 10 da zurfin kududufin 20. Akwai hanyoyin kula da kududufin lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da samun yanayin zafi ko sanyi a wurin, tare da kawar da ƙwari da ruwan sama don samun rana a muhallin da ake kiwon.