Shin ta yaya walƙiya take samuwa | Amsoshin takardunku | DW | 02.09.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Shin ta yaya walƙiya take samuwa

Bayani game da samuwar walƙiya da amfaninta ga ɗan Adam

default

Walƙiya a sararin samaniya

Tambaya: Shin ta yaya walƙiya take samuwa,kuma menene amfaninta ga ɗan Adam? Tambayar kenan da Malam ɗan Azumi Mahmud ya aiko mana daga jihar Damagaram a Jamhuriyar Nijer.

Amsa: To Mallam ɗan Azumi Walƙiya dai wani haske ne da kan fito daga samaniya, a lokacin tsawa idan ana ruwan sama. Kamar dai yadda aka sani cewa, kusan ko wanne abu yana da amfaninsa da kuma illarsa. To babu shakka ga walƙiya ma haka abin yake. Domin kuwa ƙididdiga ta tabbatar da cewa, tsakanin shekarun 1959-1994, kimanin mutane 4000 ne suka rasa rayukansu, Sannan kuma kimanin mutane 10,000 ne suka samu raunuka sakamakon walƙiya. Kuma walƙiya tana haifar da canjin yanayi wanda sakamakon haka, ya zuwa yanzu ƙididdiga ta nunar da cewa an yi asarar sama da dallar Amirka miliyan 30 a faɗin wannan duniya.

Kamar yadda masu hikimar magana suka ce, Hankaka kowa ya ga baƙinka to zai ga farinka, to ga walƙiyama abin haka yake, domin baya ga waccan illa da ta kan haifar, dan Adam ya samu ci gaba kwarai da gaske ta hanyar walƙiya. A lokaci mai tsawo, mutane sun ta yin nazari akan walƙiya domin amfani da haskenta, kuma sakamakon wannan ƙoƙari ne ɗan Adam ya gano yadda zai samar da hasken wutar lantarki. Kuma domin gano bayanai kan yanayin walƙiya da yadda take fitowa daga giza-gizai, yasa a shekarun baya masana ilimin sararin samaniya suka yi wani taro a birnin Alabama na ƙasar Amirka.

To sakamakon wannan bincike ne ma ya sa aka gano cewar, kalmar walƙiya na da alaka da canjin yanayi daga shekara zuwa shekara, kamar dai yadda wani masani a cibiyar nazarin giza-gizai ta Alabama ya faɗa, wato Mr. Hugh Christain. Kuma bincike ya tabbatar da cewa, an fi samun walƙiya a ɓangaren da ƙasa take fiye da ɓangaren da ruwa ya ke, kamar kogi ko tafki ko kuma teku. Kai a gaskiya ma dai kashi 98% na walƙiya, yana faruwa ne a ɓangaren dandaryar ƙasa da duwatsu.

Dangane da dalilin da ya sa aka fi yawan yin walƙiya a ɓangaren dandaryar ƙasa da duwatsu, Mr. Christian ya ce; mun yi imani hakan na faruwa ne saboda yanayin da ƙasa take da shi na riƙe zafi, sannan ta saki zafin cikin sauri zuwa ɗaukacin duniya. Shi kuwa ruwa yana iya riƙe zafi na tsawon lokaci mai yawa, kuma idan zai sake shi, to yana sakinsa ne a hankali.

To yanzu haka dai ana fatan cewar, sakamakon yadda masana ilimin kimiyya suka duƙufa wajen yin nazari akan walƙiya zai sa ɗan Adam ya gano waɗansu hanyoyi na warware matsalolinsa musamman ma dai yadda ake samun yanayin canjin ƙasa.