1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin Ostareliya ƙasa ce ko nahiya

Bashir, AbbaAugust 25, 2008

Taƙaitaccen tarihin Ostareliya da al'ummarta

https://p.dw.com/p/F4UR
Firaministan Ostareliya Kevin RuddHoto: picture-alliance/dpa

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito ne daga hannun mai sauraronmu a koda yaushe Malam Falalu Haruna da ke ƙasar Ruwanda .Ya ce; Dan Allah Sashen Hausa ku sanar da ni wai shin Ostareliya ƙasa ce ko kuma nahiya? Da fatan za ku ba ni tarihinta da kuma adadin al'ummar da ke zaune a cikinta.

Amsa: Ostareliya dai ƙasa ce kuma ɗaya daga cikin nahiyoyi shida da ake da su a duniya .Wato kamar nahiyar Afirka, Asiya, Turai da Amirka. Sai dai kuma daga cikin waɗannan nahiyoyi, Ostareliya ta kasance ƙaramarsu, kuma tana can ne a kudancin duniya. Ostareliya ta ƙunshi Tsuburin Tasmani tare da sauran wasu tsuburai da dama da ke tekun Indiya da Pacific. Haka kuma daga cikin ƙasashen da ke maƙwabtaka da ita akwai ƙasashen Indonesiya Estimo –Papau ,New Guinea ta ɓangaren Arewa , Solomom Island da vanautau da New Colodoniya ta Arewa maso Gabas. Sai kuma New Zealand a ɓangaren kudu maso Gabashi. A taƙaice nahiyar Ostareliya ita ce kawai ɗaya tilo da ke da ƙasa ɗaya.

Sama da shekaru dubu 24 da suka shuɗe, 'yan asalin ƙabilar Ostareliya suka fara zama a kan babban tudun ƙasar, daga baya masunta suka fara kai ziyara daga wasu wurare. Sannu a hankali aka wayi gari shekarar 1606 Turawan Jamus suka gano tsuburin. Ana nan zuwa 1770 sai Turawan ƙasar Birtaniya suka ɓulla wannan ƙasa in da kuma suka mamaye rabin ƙasar, suka ci gaba da faɗaɗa mamayarsu har sai da a ranar 26 Jan,1788 suka kai ga wurin da a yanzu ake kira da suna New south Wales.

Haka dai tafiya ta ci gaba jama'a na karuwa ana sake gano ko kuma kafa wasu garuruwan har zuwa ƙarni na goma sha tara in da aka sami ƙaruwar wasu dauloli biyar masu cin gashin kansu. A kuma farkon ƙarni na ashirin ne aka ƙara gano wata daular mai cin gashin kanta a kan biyar ɗin baya wanda kuma ya zamojanhoriya .Wannan ya yi sanadiyar kirkiro yankin renon Ingila a Ostareliya. Wato (Common Wealth Australia) . Haka kuma tun daga lokacin da ta zamanto tarayya, ƙasar Ostareliya ta ci gaba da bin tafarki irin na Dimokuraɗiyya.da shugabanci mai 'yanci. Tare kuma da kasancewa wani fage mai mahimmanci ga ƙungiyar ƙasashe renon Ingila. sunan babban birnin wannan ƙasa dai Caberre.

To haka kuma sarauniya Elzeberth ii ta ƙasar Ingila, ita ce sarauniyar Ostareliya, matsayin da ya sha banban da na mai riƙe da shugabancin ƙasashe renon Ingila. Wani abin lura kuma shi ne da akwai Gwamna Janar a wannan yanki a matakin tarayya kana kuma a matakin jihohi akwai Gwamnoni. Koda yake kuma tsarin mulkin ƙasar ya baiwa gwamna janar ɗin cikakken ikon gudanarwa amma ba zai iya zartar da komai ba sai ya tuntuɓi firaministan ƙasar.

Ƙasar Ostareliya na da jihohi 6 tare da wasu manyan birane guda biyu da kuma wasu ƙananan yankuna. Waɗannan jihohin kuwa sune New South Wales, Queens Land, South Ostareliya, Tasmaniya, Victoriya da Western Ostareliya. Mayan biranen kuma su ne yankin da ake kira Northern Teritory da kuma babban birnin Ostareliya (Australian Capital Teritory).

To dangane da batun yawan al'ummar wannan ƙasa, sakamakon ƙidayar jama'a ta shekara ta 2008 ya yi nuni da cewa akwai kimanin mutane sama da miliyan 21 da dubu ɗari uku da ke zaune a ƙasar Australia .Kuma kashi 60 bisa ɗari na waɗannan mutane, na zaune ne a manyan biranen ƙasar kamar irin su Sydney, Melbourne, Brisbane Peth da kuma Afdelaide.