1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Shin mintina nawa ne a shekara

Taƙaitaccen bayani game da yawan awanni da mintina da kuma sakan-sakan ɗin da ake da su a shekara

default

Agogo sarkin aiki

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Sama'ila Idris Saleh London, ciki junction Maiduguri Najeriya. Ya ce Deutsche Welle ku fahimtar da ni wani abu mai kamar haka; Wai shin a shekara awanni nawa ne, mintina nawa ne, kuma sakan nawa ne?

Amsa: To malam Sama'ila, ka ga dai a ƙalla akwai kwanaki 365 a shekara, kuma akwai awa 24 a kwana ɗaya. To idan kana so ka san yawan awannin da ake da su a shekara, sai ka ce kwanaki 365 sau yawan awannin da ake da su a kwana ɗaya wato awa 24. ka ga idan akai 365 sau 24 zai ba da 8,760. Wato kenan akwai awanni 8,760 a shekara ɗaya.

To idan kuma kana so ka san yawan mintinan da ake da su a shekara. Sai ka haɗa adadin awanin shekara sau yawan mintinan da ake da su a awa ɗaya. Wato ma'ana a shekara muna da awa 8,760 kuma a kowacce awa muna da minti 60. to sai a yi 8,760 sau 60. Abin da ya ba ka shi ne adadin mintinan da suke a cikin shekara. Kuma idan ka yi za ka samu cewa akwai minti 525,600 a shekara.

Haka zalika idan muka koma ga batun sakan. Ka ga dai akwai sakan sittin a kowanne minti ɗaya. To tun da mun gano yawan mintin da ake da shi a shekara, to sai mu yi adadin mintinan shekara sau adadin sakan ɗin da ke cikin minti. To kuma yanzu mun san cewa akwai minti 525,600 a shekara, sai mu yi sau 60, abin da ya ba mu shi ne adadin sakan-sakan da ake da su a shekara. Kuma idan ka yi za ka samu cewa akwai sakan 31,536,000 a shekara.

Wato a jumlace kenan idan za mu ba ka amsa sai mu ce da kai;

Akwai adadin awa 8760 a shekara. Sannan akwai adadin minti 525,600 a shekara. Sannan kuma akwai adadin sakan 31,536,000 a shekara.

Da fatan ka gamsu.