1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin menene matsayin NEPAD a Afirka

December 17, 2007

Bayani game da matsayin shirin NEPAD a Afirka

https://p.dw.com/p/Ccvu
Taron Shugabannin Afirka a Adis ababaHoto: picture-alliance/ dpa

Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, sannunmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Abdullahi Isuhu mazaunin birnin Yamai dake Jamhuriyar Niger. Malamin cewa ya yi; Shin menene matsayin shirinnan na NEPAD a Afirka, kuma me ya sa wasu Mutane da dama waɗanda suka haɗa har da wasu shugabanni a ƙasashen Afirka suke sukan wannan shiri?

Amsa: NEPAD dai shiri ne da aka ƙirƙiroshi na ƙawance tsakanin ƙasashen Afirka domin haɓakar tattalin arziƙinsu, wanda a Turance aka fi sani da suna “New Partnership for Africa’s Development” a taƙaice kuma sai a ce (NEPAD). Shi dai wannan shiri ya samo asali ne lokacin da ,Ƙungiyar Haɗinkan Afirka wato (OAU) a da, kuma (AU) a yanzu, ta baiwa wasu daga cikin shugabannin ƙasashen Afirka damar lalubo hanyoyin da za a haɓaka tattalin arzikin ƙasashen Nahiyar Afirka.

To sai dai kuma gaskiya ne cewa, Mutane da dama da suka haɗa da masharhanta da manazarta da dama akan harkokin Afirka suna sukan tsarin da ake tafiyar da wannan shiri na NEPAD.

Dr. Tajudeen Abdur-Raheem Mutum ne mai fafutukar yancin dan Adam kuma mai fafutukar ganin cewa an samu haɗaɗɗiyar gamayyar Afirka, har ila yau kuma shi ne mataimakin darakta na bangaren Afirka a shirinnan na raya ƙasashe, wato “Millennium Development Goals”. Na samu tattaunawa da shi, kasancewar yana ɗaya daga cikin Mutanen da suke adawa da tsarin da ake tafiyar da harkokin NEPAD a halin yanzu. Ga dai yadda hirar tamu ta kasance.

Bashir: Ko menene dalilin da ya sa kai da wasu masu ra’ayi irin naka kuke sukan yadda ake tafiyar da shirin NEPAD ?

Dr. Tajudeen: Abin da ya sa ni da sauran masu ra’ayi irin nawa muke sukan yadda ake tafiyar da wannan shiri shi ne. Su shugabannin Afirka sun fi sa ransu akan cewa za su samu tallafi daga ƙasashen Turai. Ni kuma a gani na yaya za a yi ƙasashen da sune suka danne mu, su suke ta cin albarkacin arzikinmu ta mulkin danniya da mallaka, to yaya za a ce wai wanda yake yi maka haka kuma shi ne zai taimake ka, ka tsaya da ƙafafuwanka? Wannan shine dalilin da ya sa a baya shugabanni irin su Obasanjo na Najeriya, irin su Mbeki na Afirka ta Kudu suka yi ta yawo ƙasashen Turai da Amirka suna cewa a taimake su-a taimake su, musamman ma ida za a yi taron ƙasashe masu arzikin masana’antu wato (G8).

Bashir: To Dr. Na ji ra’ayinku na manazarta, to amma me ya sa wasu daga cikin shugabannin ƙasashen Afirka ba su bayar da goyon bayansu ga wannan shiri ba har yanzu, duk da cewa shiri ne da aka ƙirƙiro shi domin ƙasashen Afirka gaba ɗaya?

Dr. Tajudeen: Yadda shugabannin ƙasashen da aka ɗorawa alhakin wannan aiki suka fara shi, shi ya sa wasu daga cikin shugabannin Afirka suka ƙi bayar da haɗinkai da goyon baya har yanzu.

Bashir: Ko zaka gaya mana misalin shugabannin da suka ƙi bayar da wannan goyon baya?

Dr. Tajudeen: Misali shine shugaba Mu’ammar Gaddafi na Libya, kusan a duk shugabannin da suke sukan tsarin tafiyar da wannan shiri shi ne a gaba.

Bashir: Me ya sa kuke ganin tsarin da ake bi ba zai yiwu ta hanyarsa a samu ci gaba ba?

Dr. Tajudeen: Abin da ya sa muke ganin ba zai taɓa yiwuwa a samu wani ci gaba mai ɗorewa ba a yadda suke nemansa ɗinnan shi ne, lokacin da aka yi taron kasashe masu arziƙin masana’antu a ƙasar Kanada, sun ce suna neman taimakon Biliyan Ashirin (20,000,000,000) kowacce shekara har tsawon shekaru goma. To a wannan taro na Kanada sai shugabannin turai suka ce ba zai yiwu ba sai dai a ba su Biliyan Shida (6,000,000,000), to Biliyan shida ɗin ma ba sabon alƙawari ba ne, domin dama tun tuni a kwai wannan alƙawarin, cikawa ne kawai da ba a yi ba. To ka ga tun anan suma kansu sun san ba zai taba yiwuwa ba ta hanyar da suke so.

Bashir: To duk da cewa an samu waɗannan ƙorafe-ƙorafe, amma dai hakan ba zai sa a ce ba a samu wata nasara ba. Wace nasara kake ganin an samu ta hanyar wannan shiri na NEPAD?

Dr. Tajudeen: Akwai nasara nan da can amma ba yadda ake so abin yake tafiya ba, domin kuwa yadda su shugabannin Afirkan suke yiwa junansu ɗanwaken-zagaye, idan yau an ce ga yadda za a yi abu tare, gobe sai ka ji wannan shugaba ya ware yana haɗa baki da shugabannin Turai, jibi kuma sai ka ji wancan ya ware shi ma yana nasa harkokin daban. To abin da aka ce za a yi tare amma kowa ya ware yana haɗa baki da waɗansu, ta yaya za a samu nasara.

Bashir: To yanzu Dr. ta yaya za a ceto wannan shiri na NEPAD daga cikin wannan garari da ya faɗa?

Dr. Tajudeen: Na farko dai dole sai Shugabannin Afirka sun daina munafunci. Su daina zagayewa suna haɗa baki da Turawa bayan an tsai da shawara ta gaba daya akan yadda za a tafiyar da al’amura.

Abu na biyu shi ne, ya kamata mu san cewa duk ƙasashen da suka ci gaba in ba na Turai ba waɗanda suka samu ci gabansu ta hanyar danniya da bautar da Mutane kamar yadda aka kwashi iyaye da kakanninmu, asirin ci gaban kowacce al’umma shine, su dogara da arzikin da Allah ya ba su. Kuma Allah ya albarkaci nahiyar Afirka da abin da bai albarkaci sauran nahiyoyi da su ba. Don haka matuƙar dai muka dogara da kanmu, kuma muka haɗa kanmu a matsayin al’umma daya a Afirka, to babu shakka nahiyar Afirka sai ta zama nahiya mafi ɗaukaka a wannan Duniya.