1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

SHIN ME AKE CIKI GAME DA YAKI DA YAN TAADDA DA KUMA AIKIN TAADDANCI.....

default

Masu nazarin abin da kaje yazo na ganin cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da kakkabe aikin yan taadda a doron kasa a hannu daya kuma dana yan kunar bakin wake.

Wan nan kalami dai na masu nazarin abin da kaje yazon ya samo asaline,sakamakon ire iren furucin shugaba Bush da mukarraban sa na cewa babu shakka akwai nasara kann yadda suke yaki da aikin taaddanci da kuma yan taaddda.

A misali a cewar masu nazarin abin da kaje yazon,a makon daya gabata sai da shugaban hukumar leken asirin kasar Amurka George Tenet ya bayyanawa duniya cewa akwai alamun narasa dangane da yaki da taaddanci da kuma yan taadda.

To Amma kuma a cewar manazartan a makon ne kuma yan kunar bakin wake suka kai hari a can kasar Spain,wanda hakan yayi ajali daruruwan mutane da daman gaske ban da wasu kuma da dama da suka jikkata.

A cewar manazartan,wan nan hari da aka kaiwa kasar data kasance daya daga cikin kawayen kasar ta Amurka lokacin yakin iraqi,babu shakka na nuna gazawar gwamnatin Bush a fili na rasa bakin zaren warware wan nan matsala ta aikin taaddanci da kuma yan taaddan.

Bugu da kari,a hannu daya kuma a cewar manazartan a yayin da kasar Amurka ya kamata taci gaba da laluben wanda suke zargi nada alaka da aikin taaddanci,a lokacinne kuma ta mayar da hankalinta kann iraqi.

A wan nan lokaci a cewar masu nazarin abin da kaje yazon hankalin Amurka da kawayen ta bai kwanta ba sai data kifar da gwamnatin Saddam Hussain.To amma babbar abin tambaya a nan shine,shin ina makaman nukiliyar da sukace a dalilin sana suka kai wan nan hari.

A waje daya kuma áta bakin tsohon shugaban bincike na mdd a kasar Iraqi,Hans Blix cewa yayi matakin da shugaba Bush ya dauka na danganta kasar iraqi da kungiyyar Alqaeeda ko kuma yan darkar sunni babban kuskure ne,wanda hakan ya kara dagula al,amurran siyasar kasar.

Haka shima sabon faraministan kasar Spain Jose Zapatero ya fadawa yan jaridu cewa yakar kasar Iraqi da Amurka da kawayen ta sukayi babu shakka annoba ce, dake nuni a fili cewa akwai son kai dangane da daukar wan nan mataki na yakar kasar ta iraqi daga bangaren shugaba Bush da faraminista Tony Blair na Biritaniya.

Jose Zapareto yaci gaba da cewa yakin da kasar Amurka da kawayen ta suka gudanar a iraqi babu abin da ya haifar illa rashin zaman lafiya da kyama a tsakanin al,ummar kasar a hannu daya kuma da kara kyankyashe yan taadda a doron kasa baki daya.

Rahotanni dai daga kasar ta Spain sun nunar da cewa kasar na daya daga cikin sahun gaban kasashe da suka daurewa kasar Amurka gindi na kaiwa kasar ta iraqi hari,ta hanyar bayar da gudunmawar soji 1,300 a wancan lokaci.

Daukar wan nan mataki kuwa na faraminista Jose Maria Aznar a wancan lokaci ya samu suka da rashin goyon baya daga al,ummar kasar,amma kuma duk da haka yayi kemadugus.

Yin hakan da kuma wasu dalilai na siyasar gwamnatin sa a cewar rahotanni na daga cikin dalilan daya karshi ya baro na rashin goyon bayan al,ummar kasar wajen manufar sa tayin tazarce a gadon mulkin kasar ta Spain a karo na biyu.