1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin ina siyasar Nijeriya ta dosa?

May 14, 2010
https://p.dw.com/p/NOQk
Shugaban Nijeriya Jonathan GoodluckHoto: AP

A wannan makon ma dai jaridu na Jamus sun sake mayar da hankali akan Nijeriya tare da saka ayar tambaya a game da yadda makomar siyasar ƙasar zata kasance bayan rasuwar marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar Adua. A cikin nata sharhin dai jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:

"A hukumance dai Nijeriya ƙasa ce mai bin tsarin mulkin demoƙraɗiyya dake da jam'iyyun siyasa barkatai, amma a haƙiƙatal-amari jam'iyar PDP ce take da babban angizo a siyasar ƙasar. Hakan ta sanya Nijeriya tayi kama da wata ƙasa mai tsarin jam'iyyar siyasa ɗaya tilo, inda manufofi na siyasa da tattalin arziƙi ke tafiya kafaɗa-da-kafaɗa da juna. Irin wannan yanayi ya kan yi cikas ga tsarin mulki na demoƙraɗiyya saboda akalar mulki na ci gaba ne da wanzuwa a cibiya ɗaya a kuma yi watsi da sauran cibiyoyi masu muhimmanci bisa manufa. A yanzun dai an rantsar da Jonathan Goodluck a matsayin sabon shugaban Nijeriya, amma fa muddin yana fatan ganin an tsayar da shi takarar zama shugaban ƙasa a zaɓen shekara mai zuwa to kuwa wajibi ne tun a yanzun ya fara taka rawar gani ya kuma ba da la'akari sosa akan mutumin da zai naɗa don zama mataimakinsa."

A karon farko a cikin tarihin kotun ƙasa da ƙasa akan miyagun laifuka, shi kansa babban lauya mai ɗaukaka ƙara na kotun ya ɗauki matakin gabatar da shari'a akan wasu gaggan jami'an siyasa. A lokacin da take rawaito wannan rahoto mujallar Der Spiegel mai fita mako-mako cewa tayi:

"A maimakon yadda aka saba gani a zamanin baya, inda gwamnatocin kasashe ko kuma kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya kan gabatar da ƙara gaban alƙalan kotun ƙasa-da-ƙasa akan miyagun laifuka dake birnin The Hague, a halin yanzu haka babban lauya mai ɗaukaka ƙara a kotun Luis Moreno-Ocampo na shawarar zarcewa zuwa Nairobin Kenya domin ya fara ɗaukar matakin farko na binciko ainihin masu alhakin ta'asar siyasa da zub da jinin da aka fuskanta a ƙasar a farkon shekara ta 2008, inda mutane dubu da ɗari uku suka rasa rayukansu. A saboda kasancewar gaggan 'yan siyasar Kenya da ma kotunan ƙasar sun gaza wajen lalubo masu laifukan Morno-Ocampo ya tsayar da shawarar ɗaukar matakin da kansa don zama abin koyi game da yadda ake farautar masu aikata ɗanyyen aiki, kamar yadda mujallar ta Der Spiegel ta rawaito."

Südafrika Demonstration
Masu zanga-zangar adawa da cin hanci a Afirka ta KuduHoto: AP

A daidai ranar sha ɗaya ga watan yuni mai kamawa ne da za ƙaddamar da gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya a Johannesburg ta Afirka ta Kudu. To sai dai kuma ƙasar ta fuskanci matsaloli daban-daban, a baya-bayan nan, waɗanda ba ta taɓa ganin irin shigensu ba tun bayan kawo ƙarshen mulkin wariyar jinsi a shekara ta 1994, a cewar jaridar Die Tageszeitung. Jaridar ta ci gaba da cewar:

"Afirka ta Kudu ta sha fama da zanga-zangar adawa da matsalar cin hanci da rashin taɓuka wani abin a zo a gani don kyautata makomar jin daɗin rayuwar al'uma. Tun dai misalin shekaru goma sha shida da suka wuce ƙasar ke cikin wani mawuyacin hali inda aka riƙa fargabar cewar ka da fa ta bi saun sauran ƙasashen Afirka ta faɗa cikin matsalolin nan na cin hanci da talauci da rashin iya gudanarwa. Amma a yanzun al'amura sun fara sararawa inda akawai kyakkyawan fata game da makomar ƙasar da kuma tinkarar duk wata ƙalubala da ka taso."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu