Shin da gaske ne an samu zanen siffa mai kama da fuskar mutum a duniyar ...
May 19, 2008Tambaya: Shin wai da gaske ne an samu zanen siffa mai kama da fuskar mutum a duniyar Mars? Da fatan za ku sanar da ni gaskiyar batu game da binciken da masana suka yi akan duniyar Mars. Wannan ita ce tambayar da muka samu daga hannun Malam Hassan Shugaba daga ƙasar Sudan.
Amsa: Gaskiya akwai zanen sifffa ko halittu masu kama da ta mutane a duniyar mars, domin kuwa wasu hotunan masu kama da na Indiyawan daji da aka ɗauko a duniyar Mars, sun nuna zanen fuskokin wasu halittu masu kama da mutane. Ko da yake hotunan da alamu kamar an ɗauke su ne a lokacin da rana ko dai ta fara fitowa ko kuma tana shirin faɗuwa, amma dai ya bayyana siffa ta fuskar bil'adama kwatankwacin irin alamun halittu da mukan gani ko hasashe a cikin gajimare.
Duniyar Mars ita ce duniya ta huɗu da ke kusa da rana bayan duniyar ɗan Adam daga cikin duniyoyi tara kamar yadda masana ilimin sararin samaniya suka bayyana. Kuma wannan suna nata ya samo asali ne daga wani gunkin Romawa. Haka kuma baki ɗaya girman duniyar Mars bai fi rabin girman duniyar da mutane ke zaune a ciki ba, sai dai kuma cike take da duwatsu da kwazazzabai waɗanda suka kera wanda ake dasu a duniyar ɗan Adam.
To har'ila yau kuma kwana ɗaya a duniyar Mars ya fi na duniyar ɗanm Adam da awa 12. Wato kamar yadda kowa yasan cewa awa 24 suke kwana ɗaya a duniyarmu, ita duniyar Mars awa 36 kenan ke kwana ɗaya. Hakan ne kuma yasa kwanaki 687 ne ke shekara guda a Mars, saɓanin kwanaki 365 a duniyar dan Adam.
Ikon Allah ba shi da iyaka, domin kuwa har'ila yau duniyar Mars da akwai kwazazzabai da dama masu yanayi da wutsiyar koguna to sai dai a ƙafe suke sabo da tsananin sanyi wanda ke sa duk wani abu mai ruwa-ruwa na wurin ya sandare.
To mai yiwuwa mutum ya yi tunani cewa saboda tsananin sanyin da ake batu wannan wuri na da shi, ƙila za a iya hura wuta a ji ɗimi. To ko kusa ba shi yiwuwa saboda binciken masana ya nunar da cewa, ba a samun makamashi a duniyar Mars, kuma babu nau'in iskar nan ta (Oxygen) a sararin samaniyarta. To ba ma wannan ba kaɗai, ko da mutum zai yi ƙoƙarin ɗaukar wani ɓangare na irin ƙanƙarar da ake samu a wanann duniya ya ce zai narka ta zuwa ruwa, ƙanƙarar za ta narke, to amma kuma mai makon ta zama ruwa sai ta zama iska duk dai sabo da rashin wasu sinadarai a sararin samaniyar duniyar Mars ɗin waɗanda za su ba da damar yin hakan.