Shin da gaske ne akwai kifi mai daskarewa | Amsoshin takardunku | DW | 30.04.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Shin da gaske ne akwai kifi mai daskarewa

Bayanin kifi mai daskarewa ta wata hanya ta musamman

Kifi

Kifi

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Abdullahi: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun mai sauraronmu a yau da kullum, Malama Fatima Usman daga jihar Kanon tarayyar Najeriya; Malamar cewa ta yi; Shin dagaske ne wai akwai wani kwado mai-daskarewa a cikin kankara?,to in dai da gaske ne, ina so ku sanar da ni hanyar da yake daskarewar, da kuma yadda rayuwarsa take kasancewa yayin da ya daskare da kuma bayan kankarar ta narke.

Bashir: To Kwado mai daskarewa dai, wani nau’ine daga cikin kwadin da Allah ya halitta a cikin ruwa, musamman madai a kasashe masu sanyi.Shi irin wannan kwado yana kunshe ne da wasu bakin siffofi wadanda suka sabawa tsarin rayuwar halittar dabbobi. Dalili kuwa shine,a lokacin da wannan kwado yake a daskare da kankara,baya nuna wata alama ta rayuwa a tare da shi, domin kuwa a wannan lokaci da yake a daskare,Bugun zuciyarsa da numfashinsa da kuma kewayawar jini a jikinsa, duk suna tsayawa ne cak , basa aiki.To amma yaninda kankarar jikin nasa ta narke sai kwadon ya dawo cikin hayyacinsa, kamar dai wanda ya tashi daga barci.

Abdullahi:To bisa al’ada rayayyun halittu idan suka samu kansu a hali na daskarewa, sukan fuskanci hadari mai yawan gaske, yaya batun yake ga kwado mai daskarewa?

Bashir: To babu shakka abin ba haka yake ba ga kwado mai daskarewa, domin a yayin da wannan kwado yake a cikin halin daskarewa yana dauke da wasu halittu da suke tara masa sunadarin glucose mai yawa a jikinsa ayayin da yake daskarewa.Shidai Glucose,shine yawan sikarin da yake a jikin dabbobi da mutane.Tom ga wannan kwado, adadin yawan sikarin da ke jikinsa yana da yawa kwarai da gaske, domin a wani lokaci,a cikin lita daya karfin sikarin yakan kai 550 a maaunin milimol.wanda a ka’ida ta kimiyya da aka sani a jikin kwadi, karfin sikari, bai kamata ya wuce1-5 ba,a ma’aunin milimol.Ga mutane kuwa karfin sikarin jikinsu bai kamata ya zarce 4-5 ba,a ma’aunin na milimol .Sabodahaka wancan adadi na karfin sikari 550 da ke tare da daskararren kwado inda ace a rayuwa ce da aka sani, ba’a daskare ba,to zai iya haifar da mummunar illa ga rayuwar kwadon.

Abdullahi:To menene amfanin wannan sinadari mai yawa haka a jikin wannan kwado?

Bashir: To amfanin wannan sinadari na sikari mai yawa shine, ya rike ruwa a jikin kwayoyin halitta, kuma ya kare su wadannan kwayoyin halitta motsewa, su kuma kwayoyin halittar da ke jikin fatar kwadon suna da saurin Sabo da sinadarin sukari na Glucose, saboda haka suna taimakawa sinadarin bazuwa cikin sauki.Kuma yawan wannan sinadari shine yake sanya jikin kwadon, ya rage hucin dake haifar da canjin dake afkuwa a cikin jikinsa a yayin da yake canjawa daga ruwa zuwa kankara.Bincike ya nuna cewa, shi wannan sinadari na sikari wati Glucose, zai iya ciyar da daskararrun kwayoyin halittun wannan kwado.Har ila yau a wannan lokaci, bayan shi wannan sinadari na glucose yana aiki na musamman da ruwan jiki y kamata yayi,a daya gefen kuma yana tsayar da gudanar jujjuyawar ruwa da abinci don kada suyi saurin Narkewa su kare da wuri.

Abdullahi:Ta ina irin wannan sunadarin sikari na glucose mai yawan gaske, ya samu haka kwatsam a jikin wannan kwado?

Bashir: To Abdullahi, Amsar na da ban sha’awa : Shi wannan nau’i na kwado mai daskarewa, wata halitta ce da aka shirya mata wadannan kayan aiki na musamman don su gudanar da wannan aiki.To a Yayin da kankara ta sauka a fatar jikin wannan kwado, sai sako ya tafi cikin hanta. Ya sanar da ita cewa , ta juyar da wasu daga cikin sunadaran glycogen dinta zuwa sunadaran sukari na glucose.Ko dadai Yanayin tafiyar wannan sako zuwa hanta abu, ne boyayye. To a cikin Minti biyar kacl da zuwan sakon, sai yawan sukarin dake cikin jinin kwadon ya rika karuwa:

Maganar gaskiya itace, babu shakka, Ba tare da wata tambaya ba, dabbar da aka sanya mata irin wadannan kayan aikin dake canza yanayinta, don ta jure da yanayin da zata samu kanta a ciki,yafi karfin ace wannan tsarine da ya samu hakkannan bagatatan, Illa dai kawai dole a yarda da cewa, akwai wani mahalicci kuma mabuwayi a cikin ikonsa, da yake tafiyar da wannan al’amari, ta hanyar tsarin da babu karyewa a cikinsa.

Babu wani tsautsayi ko haduwar yanayi ko kuma juyin halitta da zai iya samarda irin wannan gawurtaccen tsari, sai Allah mahalicci, mabuwayi,madaukaki kuma mai iko akan komai

 • Kwanan wata 30.04.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvUq
 • Kwanan wata 30.04.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvUq