1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin an samu ci gaba a muradun ƙarni?

September 24, 2010

Bisa ga ra'ayin jaridar Die Tageszeitung shugaba Jonathan Goodluck ya karya alƙadarin jita-jitar da ake yi game da tsayawarsa takarar zaɓe

https://p.dw.com/p/PLwF
Shelkwatar Majalisar Ɗinkin Duniya a New YorkHoto: AP

Ko da yake taron ƙolin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ɗauki nauyin gudanarwa akan burin nan na ƙarni a birnin New York shi ne ya fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon, amma a ɗaya ɓangaren sun leƙa sassa daban-daban na Afirka domin duba halin da ake ciki..Misali dai jaridar Die Tageszeitung dake cewar:

"Shugaban Nigeria Jonathan Goodluck ya fasa ƙwai sakamakon sanarwar da ya bayar ta yanar gizo game da niyyarsa ta tsayawa takarar zaɓen shugaban ƙasa da aka daɗe ana jita-jita akai. Shugaban, wanda ya gaji ragamar mulki daga marigayi Alhaji Umaru Musa 'yar Adua a cikin watan fabarairun da ya wuce, ya ba da wannan sanarwar ne a daidai lokacin da tsofon shugaban mulkin soja Ibrahim Babangida ke ƙoƙarin gabatar da yaƙinsa na neman zaɓe tare da wani gagarumin biki na siyasa. Shi dai Babangida yana zaman wani tsofon hannu ne a siyasa, a yayinda shi kuma Jonathan ke kallon kansa tamkar Obaman Nijeriya."

Nigeria Jonathan Goodluck
Shugaba Jonathan Goodluck na NijeriyaHoto: AP

Kimanin mutane miliyan dubu ɗaya da ɗari biyar ne ba su da wutar lantarki a sassa daban-daban na duniya, wanda kuma hakan ke hana samun ci gaban tattalin arziƙi, a cewar jaridar Süddeutsche Zeitung. Jaridar ta ƙara da cewar:

"Nahiyar Afirka ita ce ta fi fama da raɗaɗin ƙarancin wutar lantarki, inda kimanin kashi tamanin cikin ɗari na mazauna yankin Afirka kudu da hamadar Sahara suka dogara kacokam akan itatuwa don samun ƙiraren wuta. Wani bayanin ma nuni yayi da cewar gaba ɗaya yawan wutar da nahiyar Afirka ke aiwatarwa baki ɗayanta ya zo daidai ne da na birnin New York a ƙasar Amirka. A sakamakon ƙarancin wutar lantarkin akasarin mutane suka zama tamkar 'yan rakiya ne kawai a al'amuran ci gaban tattalin arziƙi."

Majalisar Ɗinkin Duniya ta damu da hali na ɗarɗar da ake ciki a ƙasar Sudan, domin kuwa nan ba da daɗewa ba ake sa ran cewar kudancin ƙasar zata sanar da ikon cin gashin kanta, amma kuma fadar mulki a Khartoum ba zata yarda ta kakkaɓe hannuwanta daga albarkan man fetir da Allah Ya fuwace wa yankin ba, kamar yadda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rawaito, inda take cewa:

"Ta la'akari da haka bai zama abin mamaki ba kasancewar gwamnati a Khartoum tana maraba da duk wanda ya ta da ƙayar baya ga ƙungiyar SPLM. Domin kuwa idan har aka wayi gari saɓani na ƙabilanci, wanda a zamanin baya ya sha halaka dubban mutane a kudancin Sudan fiye da arewacinta, ya ɗauki sabon salo na yaƙin basasa, fadar mulki ta Khartoum zata iya fakewa da guzuma domin ta harbi karsana, inda zata iya tura sojojinta da iƙirarin tabbatar da doka da oda a yankin."

Brüchiger Frieden im Südsudan - Überreste eines Panzers
Ƙwarya-ƙwaryar zaman lafiya a kudancin SudanHoto: DW

"Ba girin-girin ba tayi mai", wanda shi ne take wani rahoto da jaridar Berliner Zeitung ta gabatar dangane da taimakon raya ƙasashen Afirka tana mai ba da la'akari da jawabin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tayi wa taron ƙolin Majalisar Ɗinkin Duniya akan burin nan na ƙarni a birnin New York a wannan makon. Jaridar ta ce Merkel tayi daidai inda ta nuna cewar ba yawan taimakon ake buƙata ba, abu mai muhimmanci shi ne nagartar taimakon ta yadda kwalliya zata mayar da kuɗin sabulu bisa manufa.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu