Shin akwai shukar da take iya farautar Kwari | Amsoshin takardunku | DW | 29.10.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Shin akwai shukar da take iya farautar Kwari

Bayani akan yadda shuka take farauta a wuri daya

Wata shuka mai kama Sundew

Wata shuka mai kama Sundew

Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, sannunmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.

Maidawa: Fatawarmun ta wnnan makon ta fito daga Hannun Malama Asma’u Muhammad daga Jihar Kano a Tarayyar Najeriya. Malamar tana tambaya ne game da cewar; Wai shin akwai wata shuka da take iya farautar Kwari?

Bashir: To Shukar Afrika ta kudu mai suna Sundew, Wata halitta ce daga nau’ukan tsirrai da Allah madaukakin Sarki ya halitta bisa hikima da ikonsa. Shi ‘Al-Khaliku’ ya fi kowa sanin dalilinsa na tsara dabi’un wannan tsiro a yadda yake, to amma ba shakka akwai ayoyi da hikimomi masu yawa tattare da irin tsari na musamman da wasu mu’ujizozi da Allah ya kebanci shukar sundew da su, wanda dole hankali ya yarda cewa Allah ya yi ta ne don ta zamo ayoyi, kuma abin lura da tunani ga mutane.

Wannan shuka ta sundew da yake bata da suna a Hausa, wala Allah ko don bamu san ta bane, dole sai dai mu kira ta da sunanta na turanci. To ita wannan shuka ta sha bamban da duk wasu halittu na tsirrai da Allah Ta’ala ya halitta, domin salonta, hikimominta, da tsarin farautar ta , suna bayyana zunzurutun iko da iyawar Allah ne, a gefe guda kuma suna fassara Mu’ujizozi da fifikonta bisa sauran tsirrai da Allah Buwayi, gagara misali ya halitta. Da yawa daga cikin dabbobi da tsuntsaye da tsirrai suna da wata baiwa ta hali ko dabi’a ta musamman, wanda bisa nazari dan Adam zai iya daukar darasin rayuwa a cikinta.

Dangane da yadda wannan shuka ta Sundew take samun abincinta shine; Allah Madaukaki ya baiwa wannan shuka wata Dama ta yin farauta a wuri daya . yadda take wannan farauta kuwa shine; tana kama kwari da maganadisun gashin jikinta. Ganyayyakin dake jikin shukar suna da tsawo, da kuma jan launi. A kan gashin ta kuwa akwai wani ruwa mai yauki dake fitowa wanda yake da kamshi. To kamshin wannan ruwa ne, yake jawo kwari su sauka a jikin shukar. Wata sifa ta wannan ruwa ita ce ta kasancewarsa mai yauki da danko kwarai da gaske.Yayin da wani kwaro ya tafi jikinta saboda kamshin da ya jiyo na wancan ruwa, yana sauka a kanta sai ya makale a jikin dankon. Nan da nan sai ganyen ya rufe kansa da kwaron da ya ke makale da shi, sai shukar ta muttsike kwaron, kuma sai ta fitar da duk irin sunadaran da take bukata a jikin kwaron bayan ta mutstsuke shi. Ta hakane irin wannan shuka take samun abincinta domin ta rayu.

Tsirran Sundew sun warwatsu a Duniya, suna da siffofi da kuma yanayin girma daban-daban, kuma za’a iya samun su ko’ina cikin Duniya. Suna iya jure canjin yanayi daban-daban, amma dai sun fi yi a kasashen da suke da yanayin raba mai yawa.Don a kasar Afrika ta kudunma, sukan sha wahala a lokacin da aka samu fari na yanayi.

Gaskiyar batu, Babu Mutumin da zai iya hana kansa yin mamaki yayin da ya ga lokacin da wannan shuka take rufe kanta da wannan kwaro da kuma yadda take muttsike shi. Babu shakka shukar da ke dauke da wannan fasaha , gashi bata motsawa daga wurinta, hakika wata shaida ce ta tsari na musamman. Abu ne mai wahala ace shuka ta samu irin wannan dabara ta farauta daga cikin hankalinta ko ikonta, ko kuma haka nan kwatsam wannan dabara tazo mata. Haka kuma, yana da wahala mutum ya rufe idonsa ga barin wanzuwar kadaitaccen mahalicci wanda ya sanya wa wannan shuka irin wannan aiki.

 • Kwanan wata 29.10.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/C169
 • Kwanan wata 29.10.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/C169