1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shimon Peres ya fara samun sauki

Ahmed SalisuSeptember 15, 2016

Likitocin tsohon shugaban kasar Isra'ila Shimon Peres sun ce ya fara nuna alamun samun sauki bayan da ya gamu da mutawar rabin sashin jiki a ranar Talatar da ta gabata.

https://p.dw.com/p/1K3Cr
Israel Schimon Peres
Hoto: Reuters/B. Ratner

Guda daga cikin likitocin wato Rafi Walden ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar tsohon shugaban na iya motsa kafarsa da hannu to amma har yanzu da taimakon na'ura ya ke iya numfashi kuma ba ya iya yin magana. Firamininistan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ya ziyarce shi a asibiti a jiya Laraba ya ce al'ummar kasar sun ji dadin labarin da aka samu na alamun saukin da Mr. Peres ya ke nunawa.