SHIGAR TURKIYYA CIKIN KUNGIYAR HADIN KAN TURAI. | Siyasa | DW | 26.02.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

SHIGAR TURKIYYA CIKIN KUNGIYAR HADIN KAN TURAI.

Jami'an kungiyar Hadin Kan Turai da ke birnin Brussels, suna mamakin yadda jam'iyyun siyasar Jamus ke ta muhawarar da a nasu ganin, ba ta da wata ma'ana, game da neman shiga cikin kungiyar da kasar Turkiyya ke yi. Tuni dai, kungiyar Hadin Kan Turan, ta tsai da shawarar bai wa Turkiyyan damar zamowa mambanta, muddin ta cika duk ka'idojin da aka shimfida mata, inji Günter Verheugen, kwamishinan kungiyar mai kula da harkokin karbar sabbin mambobi. Tun kusan shekaru 40 da suka wuce ne dai, ake ta tattaunawa kan batun shigar Turkiyya cikin kungiyar. A shekarar 1999 ne kuma, aka yarje kan cewar kasar za ta iya mika takardunta na neman zamowa mamba. Sabili da haka, inji Verheugen, ba batun yiwuwar karbar Turkiyyan ne ke da muhimmanci a halin yanzu ba. Abin da ake ta korafi a kansa shi ne lokacin da za a karbe ta da kuma sharuddan da ake bukatar ta cika, kafin ta sami shigowa cikin kungiyar. A cikin watan Satumba mai zuwa ne dai, Hukumar da Verheugen din ke yi wa jagoranci, zai gabatad da rahotonsa, wanda zai tabbatar ko Turkiyyan ta cika duk sharudda, kafin a fara tattaunawar da ita. Idan rahoton ya amince da bayanan da Turkiyyan ta gabatar, to a cikin watan Disamba ne kungiyar Hadin Kan Turan za ta ba ta takardar shaida, ta cancantar zamowa mambanta. Bayan hakan ne kuma za a fara tattaunawa bisa manufa, don tsai da lokacin da Turkiyyan za ta sami shiga cikin kungiyar. Duk kasashen da aka yi irin wannan tattaunawar da su a da dai, sun zamo cikakkun mabobin kungiyar. Sai dai, tsawon lokacin tattaunawar ne ya bambanta daga kasa zuwa kasa.

A nan Jamus dai, jam'iyyun siyasa sun mai da wannan batun daya daga cikin muhimman jigoginsu na yakin neman zaben shiga Majalisar Turai, wanda za a gudanar a cikin Yuni mai zuwa. Amma a kashin gaskiya, batun neman shiga kungiyar da Turkiyya ke yi, ba shi da wata alaka da zaben. Sai cikin watan Satumba, watanni 3 bayan an gama zaben ne, za a gabatar wa sabuwar Majalisar Turan, rahoton binciken da Hukumarta ta gudanar kan cancantar kasar Turkiyyan.

Sabili da haka ne kuwa, wasu masharhanta ke ganin cewa, shelanta zaben Majalsar Turan, tamkar zaben raba gardama kan shigar Turkiyya cikin kungiyar, da jam'iyar CSU ke yi, ba ta da wani tushe. An dai tsai da shawara da kuma shimfida sharudda, wadanda idan Turkiyyan ta cika su, to babu kuma wani shingen da zai hana ta shiga cikin rukunin kasashen Tarayyar Turan. A zayyane dai, shugabannin wasu kasashen kungiyar za su iya sake shawara kan wannan batun. Amma hana Turkiyyan zamowa mamba zai yi wuya, saboda tana samun cikakken goyon baya daga Jamus, da Birtaniya da Spain da kuma Italiya. daya shingen da zai iya hana mata ruwa gudu, shi ne rikicin kasar Cyprus. Amma a nan ma, bisa dukkan alamu za a iya wartware matsalar kafin shigar Cyprus din cikin kungiyar Hadin Kan Turan a cikin watan Mayu mai zuwa.

Akwai dai wasu kasashen da har ila yau ke dari-dari da karbar Turkiyya cikin kungiyar. Wadannan kuwa sun hada ne da kasashen Skandinaviya, da na gabashin Turai da kuma Faransa.

Amma a taron da ministocin harkokin wajen kungiyar suka yi a cikin watan Oktoban bara, sun amince da fadada kungiyar har zuwa wasu kasashen da ke nesa da Turkiyyan ma, kamarsu Ukraine, da Moldaviya, da yankunan bahar Rum da kudancin Kaukasus. Bisa wannan yarjejeniyar dai, kungiyar za ta iya kunsar yankuna da ke da yawan jama'a kusam biliyan daya, a cikin `yan shekaru masu zuwa.

Ashe kuwa, idan ana son a cim ma wannan gurin, to karbar kasar Turkiyya cikin kungiyar, za ta kasance wani mataki ne na share fagen cim ma babbar manufa, amma ba na iyakace fadada ta ba.
 • Kwanan wata 26.02.2004
 • Mawallafi Yahaya Ahmed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvlf
 • Kwanan wata 26.02.2004
 • Mawallafi Yahaya Ahmed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvlf