Shekau na Boko Haram ya ce tashi ta kare | Labarai | DW | 24.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shekau na Boko Haram ya ce tashi ta kare

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya nuna karaya tare da mika sako ga mabiyansa a cikin wani sabon bidiyo da ya fitar tun bayan da ya yi mubaya'a ga IS.

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da wani sabon bidiyo saboda tabbatar da cewar ya na raye sabanin hasashen da aka yi ta yayatawa a baya. Ya dai bayyana cikin yanayin rashin kuzarin da aka sanshi da shi, a inda ya yi amfani da Larabci da Hausa wajen bayyana sakon da ya ke dauke da shi.

Baya ga gaisuwa ga 'ya'yan Boko Haram, Abubakar Shekau ya kuma nunar da cewar karshenshi ya zo kusa. Sojojin Najeriya sun sha ikirarin cewra sun kasheshi. Rabon Shekau ya fito da bidiyo, tun bayan bayan da kungiyar Boko Haram ta yi mubaya'a da kungiyar IS a shekarar 2015.

Ba a dai tabbatar da sahihancin wannan bidoyi ba har i zuwa yanzu. Dubban mutane ne ke ci gaba da rasa rayukansu a Najeriya da Nijar da Chadi da kamaru tun bayan da Kungiyar ta Boko haram ta fara kaddamar da hare-hare a wadannan kasashe,