Shekaru uku bayan kawar da gwamnatin Saddam | Labarai | DW | 09.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shekaru uku bayan kawar da gwamnatin Saddam

A yau kasar Iraqi ta yi bikin cika shekaru uku da faduwar gwamnatin Saddam Hussaini, inda daruruwan yan shiá suka rika baiyana farin ciki da hambarar da tsohon shugaban daga karagar mulki. Yan Shiár wadanda suka yi dandazo a Bagadaza babban birnin kasar na dauke da katon hoto Saddam inda aka rubuta faduwar shugaban kama karya. Tare da sowa da yabon P/M Ibrahim al-Jaafari masu zanga zangar sun kuma tunato da kisan gillar da aka yiwa wani shahararren malamin shiá Mohammed Baqr Sadr a zamanin mulkin Saddam Hussaini. A bangare guda kuma yan sunni wadanda suka kasance masu fada a ji a karkashin mulkin Saddam sun Allah wadai da kasancewar sojojin kasashen ketare a cikin Iraqi wadanda suka sun haddasa rikicin addini a kasar. Jamiíyar Islama wadda kuma ita ce babbar jamíya ta yan sunni ta baiyana mamayen da sojin Amurka suka yiwa kasar Iraqi da cewa ya maida kasar dandalin balaí. Majalisar majalisar malaman Iraqin ita ma ta baiyana mamayen da cewa ya lalata kasar baki daya.