Shekaru biyar na dakarun jamus a Afganistan | Siyasa | DW | 12.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekaru biyar na dakarun jamus a Afganistan

A ranar 14 ga wata ne dakarun jamus ke cika shekaru 5 a kasar Afganistan

Dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa a Afganistan

Dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa a Afganistan

Tun daga ranar 14 ga watan janairun shekarata 2002 ne yansandan Afganisatan da hadin gwiwan dakarun jamus ,suka fara aikin gudanar da sintiri a titunan birnin Kabul,akarkashin shirin dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa dake Afganistan,da ake kira ISAF,dake aiki asassa daban daban na kasar.

Idan zaa iya tunawa , tun aranar 27 ga watan Nuwamban shekarata 2001 ne,wakilan manayan jammiyyun siyasa guda hudu daga Afganisatan suka gudanar da wata tattaunawa a Petersberg da Bonn,inda suka tattaunawa makomar wannan kasa a siyasance.Wadda ta jagorancesu ga rattaba hannu a dangane da yarjejeniyar hadin gwiwa.

To sai dai duk da cimma wannan yarjejeniyar kasar ta Afganistan na bukatar tallafin dakarun kiyaye zaman lafiya na kasashen ketare,domin cimma manufofinta na samarwa alummomin kasar rayuwa madaidaiciya.

Kasar ta Asfganistan dai na fama da rigin gimu na kabilanci daga yanki zuwa yanki,tare da sabbin tashe tashen hankula tun bayan da sojojin hadin gwiwa akarkashin jagorancin Amurka suka kaddamar da wani somame dake da nufin zakulo sauran yan gwamnatin taliban dake mulkin kasar a baya da kuma yan kungiyar alqaida.Adangane da hakane aka zartar da batun tura dakarun kiyaye zaman lafiyan kasa da kasa a biranen kasar ta Afganistan.

Bisa ga wannan komitin suhun mdd aranar 20 ga watan Disamban shekarata 2001 ya zartar a karkashin doka ta 1386,ya zartar da tura dakarun na kasa da kasa da ake kira ISAF a takaice,wadanda zasu taikamakawa harkokin tsaro a wannan kasa.

Wadannan dakaru na kasa da kasa nada alhakin tabbatar da tsaro wa gwamnatin dake da matsugunninta a Kabul,tare da samarda kaeriya wa kungiyoyin bada agaji na majalisar dunkin duniya dake aiki a wannan kasa.Wayannan dakarun soji wadanda yawansu yakai kimanin dubu 4 daga kasashe 18,sun kasance ne a karkashin jagorancin kasar Britania,kafin jamus ta karbi ragama.

To sai dai shekaru biyar da girke wayannan sojojin na tabbatar da zaman lafiya na kasa da kasa ko yaya alummomin kasar suke ganin tasirin su?Mr Karim Wahidi maaikacin gwamnati a birnin kabul

"A nawa ganin kasashen duniya sun mike tsaye na ganin cewa zasu taimaka wajen kawo karshen yakin na Afganistan.Muna fatan cewa a kwana a tashi zaa cimma wannan buri da aka sanya gaba.

Jamus dai tana da dakarunta kimanin 2,900 daga cikin dakaru dubu 33 daga kasashe 37 dake aikin tabbatar da lafiya ana kasa da kasa a Afganistan,wadanda kuma ke kula da harkoki a kabul da yankin arewacin kasar.

Kudancin Afganistan din dai yafi fuskantar tashe tashen hankula.richard Nugee shine kakakin Dakarun kasa da kasa ta ISAF....

"A ganina wannan shine babban kuskure da mukayai,kuma zamu yi kokarin ganin cewa baa samu asaran rayukan fararen hula ba a shekara mai zuwa".