Shekaru biyar da harin Madrid | Siyasa | DW | 11.03.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekaru biyar da harin Madrid

Kimanin mutane metan ne suka rasa rayukansu sakamakon harin na 11 ga watan Maris ɗin shekara ta 2004.

default

Pilar Manjon, shugabar ƙungiyar waɗanda harin Madrid ya shafa

A daidai ranar 11 ga watan Maris na shekara ta 2004 ne wasu 'yan ta'adda suka kai hare-hare akan wasu jiragen ƙasa guda huɗu da suka cika makil da fasinjoji dake kan hanyarsu ta zuwa bakin aikinsu a birnin Madrid na ƙasar Spain. Tare da wannan harin nahiyar turai ta shiga rukunin yankunan dake fama da barazanar hare-haren 'yan ta'adda a duniya.

Kimanin mutane metan ne suka rasa rayukansu sakamakon harin na 11 ga watan Maris ɗin shekara ta 2004. Kuma shekara ɗaya bayan haka aka sake kai wani sabon harin a birnin London wanda ya halaka mutane sama da 50, a daidai ranar 7 ga watan yulin shekara ta 2005. Gwamnatocin ƙasashen biyu, Birtaniya da Spain, a lokacin da aka kai musu hare-haren na ta'addanci suna goyan bayan yaƙin da tsofon shugaban Amurka George W. Bush ya gabatar akan Iraƙi. Kuma ko da yake tsautsayin hare-haren ya rutsa ne da mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba, amma akasarin mutane na tattare da ra'ayin cewar 'yan ta'addan sun ɗauki wannan mataki ne don ladabtar da ƙasashen biyu. Sai dai kuma tsofon ministan cikin gida na Birtaniya a wancan lokaci Jack Straw yayi fatali da wannan iƙirarin inda yake cewa:

"´Yan ta'adda sun kai hare-harensu a dukkan sassa na duniya, a ƙasashen da ƙawance da Amurka suke kuma mara mata baya a yaƙin Iraƙi da kuma waɗanda ba su da wata hulɗa da yaƙin Iraƙin. Sun kai hari a Kenya da Tanzaniya da Indonesiya da Yemen. 'Yan ta'addan na madalla da duk wani uzuri ko wata hujjar da za a bayar a game da matakansu na ta'adda."

Wannan bayanin na Jack Straw na yin nuni ne da kasancewar Jamus, wadda ta fito fili tana mai adawa da yaƙin Iraƙin ma sai da ta fuskanci barazanar kai mata harin da ya ci tura a shekara ta 2005. Abu ɗaya dake akwai dai shi ne tun bayan harin na 11 ga watan Maris na shekara ta 2004 matakan ta'addancin na masu zazzafar aƙidar addini ya ratsa nahiyar Turai. A martanin da ya mayar dangane da harin na Madrid a wancan lokaci, tsofon ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer cewa yayi:

"Wajibi ne mu yi mu natsu mu kuma nuna juriya. Kuma wannan maganar ba ta nufin mu riƙa sukuyar da kanmu, a maimakon haka wajibi ne muyi dukkan iyawarmu domin ɗaukar matakan kariya da riga-kafi bai ɗaya. Ko kaɗan bai kamata mu saduda ga 'yan ta'adda ba."

Daga bisani dai ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Turai sun tsayar da shawarar ƙarfafa haɗin kan ayyukan hukumominsu na 'yan sanda da leƙen asiri, inda aka naɗa Gijs de Vries, ɗan ƙasar Netherlands a matsayin jami'in ƙungiyar mai haɗa kan matakan yaƙi da ta'adda. Sai kuma da ya fito fili yayi gargaɗin cewar bai kamata a samar da wani yanayi na firgita mutane a game da musulmi ba. To sai dai kuma tun bayan gabatar da matakan yaƙi da ta'addanci ake fama da ƙorafi a game da tsawon lokacin da za a ci gaba da tara bayanai akan ɗaiɗaikun mutane da bin diddigin kai da komonsu. Da yawa daga masu fafutukar kare haƙƙin al'uma na tattare da ra'ayin cewar matakan ba kome ba ne illa wani mataki na neman fakewa da guzuma domin a harbi karsana, inda mahukunta zasu samu saƙin leƙen asirin jama'a, wanda ba lamari ne da za a daddara da shi ba.

Mawallafi: Christoph Hasselbach/Tijani Lawal

Edita: Mohammad Awal