Shekaru 800 da kafa garin Dresden | Zamantakewa | DW | 31.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Shekaru 800 da kafa garin Dresden

Bana ake bikin samun shekaru 800 da kafa garin Dresden mai dadadden tarihin al'adu a gabacin Jamus

bikin shekaru 800 ga Dresden

bikin shekaru 800 ga Dresden

Manufar matakin da gwamnati ta dauka na yi wa garin na Dresden gyarar fuska yana da nufin sake dawo masa da martabarsa ta tarihi da al’adu a tsakanin biranen Jamus. To sai dai kuma zai dauki wasu karin shekaru nan gaba kafin garin ya koma kann suffarsa ta asali duk da cewar bana ne yake bikin samun shekaru 800 da kafuwa. Akalla dai an samu kafar kammala kwaskwariman da ake wa babbar fadar sarakunan gargajiya, wanda a sakamakon bannatar da ita da aka yi a yakin duniya na biyu aka mayar da ita tamkar rumbun adana amfanin noma irinsu dankalin turawa da ragowarsu. A lokacin da yake bayani game da haka Dr. Claus Kemmer, jagoran maziyarta masu yawon bude ido a garin Dresden cewa yayi:

„An fara yi wa babbar fadar gyaran fuska ne a shekara ta 1986. A wancan lokaci ne aka sabunta rufin fadar da tagoginta. To sai dai kuma ba’ada bayan haka ba a ci gaba da aikin ba.“

A dai halin da ake ciki yanzun an sabunta fadar domin mayar da ita kann suffarta ta shekarar 1733. Dubban daruruwan maziyarta ke kwarara zuwa fadar domin nakaltar dakunan da aka kebe domin ajiye kayan tarihi a cikinsu. Dr. Claus Kemmer ya kara da bayani yana mai cewar:

„Abin da ake fatan yi shi ne mayar da fadar wani kasaitaccen gini na ajiye kayan tarihi a cikin shekaru goma masu zuwa, ta yadda abin zai yi daidai da dmbim maziyartar dake kwarara zuwa garin Dresden mai dadadden tarihin al’adun Jamus.“

A cikin kiftawa da Bisimillah aka yi kaca-kaca da garin na Dresden, wanda tsofon sarkin sarakunan yankin August tare da dansa suka yi kimanin shekaru 60 suna masu kokarin mayar da shi wani yankin dausayi tsakanin kasashen Turai. A dai halin da ake ciki yanzu an samu kafar warkar da da yawa daga tabon da yakin cacar baka tsakanin kasashen gabaci da na yammacin duniya ya haddasa tare da sake maidowa da garin Dresden martabarsa. A watan nuwamban shekara ta 2001 aka sake bude gidan ibadar Yahudawa dake kurkusa da babbar fadar. Kuma a halin da ake ciki yanzu haka shi ne cibiyar sarrafa na’ura mai kwakwalwa a duk fadin duniya, kazalika wata cibiyar binciken fasaha mai zurfi a Jamus baki daya.

An dai shirya shagulgula da bukukuwa da kuma taruka sama da 250 tsawon wannan shekarar dangane da murnar cika shekaru 800 da kafuwar Dresden mai cike da tarihin al’adun Jamus.